in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana shirin da Sin ta yi na yin kwaswakarima kan hukumomin kasar
2013-03-11 15:50:00 cri

Yau Litinin 11 ga wata a nan birnin Beijing, cibiyar yada labaru, ta taro na farko na majalisar wakilai ta 12 na jama'ar kasar Sin ta kira wani taron manema labaru, inda mataimakin shugaban ofishin kula da tsarin hukumomin kasar Sin Wang Feng ya amsa tambayoyin da aka gabatar masa kan shirin yi wa hukumomin majalisar gudanarwa kwaswarima, da canja ayyukansu, da dai sauran abubuwan dake da alaka da wannan batu.

Wang Feng ya ce, muhimmin aikin da aka sa gaba a wannan karo, dangane da yin kwaskwarima shi ne, rarrage yawan hukumomi da saukakke ikonsu, wato baiwa kananan hukumomi damar gudanar da ayyuka da kashin kansu, da kuma yi amfani da karfin al'umma ta fuskar harkokin da suka shafe su, ta yadda za a warware tarin matsaloli, a kuma baiwa gwamnati zarafin kulawa da ragowar muhimman harkokin da suka dace.

Wang Feng ya kara da cewa, an aiwatar da kwaskwarimar ne, da zummar kyautata ayyukan da gwamnatin ke yi na yin kwaskwarima da sa ido kan manyan sauye-sauye, da tafiyar da ayyukanta yadda ya kamata a fannoni hudu, wato samar da daidaito ta fuskar tattalin arziki, da sa ido ga amfanin kasuwanni, da barin al'umma ta daidaita harkokinta da kanta, da kuma samar da hidima ga jama'a. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China