in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ba ta da hakikanin tsari dangane da zuba jari ga kasashen waje, in ji Chen Deming
2013-03-08 14:50:41 cri

A gun taron manema labaru da aka yi yau Jumma 8 ga wata a nan birnin Beijing game da taron farko na majalisar wakilai na 12 na jama'ar kasar Sin, ministan cinikayya na kasar Sin Chen Deming ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ba ta fitar da wani cikakken tsari kan zuba jari a kasashen waje ba inda ya kara da cewa kamfanonin kasar Sin sun sayi wasu masana'antu bisa moriyar kansu ne.

Haka kuma, kamfanonin na dogaro da kansu wajen yanke shawarar inda za su zuba jari, da ma irin fannin da za su zuba jarin.

Chen Deming ya ci gaba da cewa, yawan kudin da Sin ta zuba a kasashen waje ya karu sosai har ya kai dala biliyan 77.2, wanda ya sa Sin ta kasance babbar kasa ta 5 wajen zuba jari a kasashen waje, a wannan shekara da muke ciki kuma Sin za ta ci gaba da samun saurin karuwa a wannan fanni.

Ban da haka, Chen Deming ya yi suka ga wasu mambobin majalisun kasashe masu wadata wadanda har ila yau suke daukar yunkurin "tinkarar duniya" da kamfanonin kasar Sin ke yi bisa tunanin kuskure na yakin cacar baki.

A sa'i daya kuma, Chen Deming ya bayyana cewa, a wani lokaci a baya, rarar kudin da Sin ta samu ta fuskar cinikayya ya taba kai kashi 6 cikin dari bisa dukkan GDP na kasar, amma a cikin shekaru biyu da suka gabata, wannan adadin ya yi kasa zuwa kashi 3 cikin dari, wanda kuma ya samu amincewa daga kasashen duniya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China