in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya nuna yabo ga samun karuwar tattalin arzikin Sin na kashi 7.8 bisa 100 a bara
2013-03-06 15:34:21 cri
A gun taron manema labaru na taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 da aka gudanar a ranar 6 ga wata, shugaban kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Zhang Ping ya nuna yabo ga yadda aka samun karuwar tattalin arzikin Sin da kashi 7.8 bisa 100 a bara.

Zhang Ping ya bayyana cewa, yawan kudin da aka kashe a kasar Sin a shekarar bara ya fi jarin da aka zuba a fannin raya tattalin arzikin kasar. Kamata ya yi a ci gaba da kiyaye muhimmiyar rawar da yawan kudin da aka kashe ya taka yayin da ake inganta tattalin arzikin kasar. Kana habaka bukatun cikin gida shi ne jigon raya tattalin arzikin kasar, kuma dole ne a tsaya tsayin daka kan shi.

Hakazalika Zhang Ping ya nuna cewa, zuba jari shi ma ya taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga samun ci gaban tattalin arzikin. Kasar Sin kasa ce mai tasowa, tana kuma kokarin raya masana'antu, birane, sadarwa, kauyuka da dai sauransu, don haka tana bukatar jarin da aka zuba gare ta.

Ban da wannan kuma, Zhang Ping ya bayyana cewa, a shekaru 5 da suka wuce, ana kiyaye samun bunkasuwar tattalin arziki a kasar Sin, yawan GDP wato kudin da aka samu daga sarrafar dukiyar kasar a shekarar 2008 ya kai fiye da Yuan biliyan 30000, yawansu a shekarar 2010 ya zarce Yuan biliyan 40000, kuma yawansu a shekarar 2012 ya wuce biliyan 50000. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China