Mr. Zhang Zhijun, ya bayyana hakan ne gabanin shigarsa babban dakin taron jama'ar kasa da ke birnin Beijng, inda aka bude taron farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 a yau Talata 5 ga wata. Zhang Zhijun ya kuma jadadda cewa, kasar Sin ba za ta canja matsayinta kan batun tsibirin na Diaoyu ba.
Haka zalika, ya kuma nuna cewa, kasar Sin za ta karfafa ayyukanta da suka shafi teku, ciki hadda bunkasa tattalin arzikin teku, da kiyaye muhallin teku, da kiyaye ikon kasar kan teku yadda ya kamata, baya ga ci gaba da kare dokokin teku. (Maryam)