in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)An bude taron farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin
2013-03-05 12:10:13 cri

A ranar 5 ga wata da safe ne aka bude taron farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, inda shugaba Hu Jintao, da Xi Jinping da sauran shugabannin kasar Sin, da kuma wakilan jama'ar kasar kimanin dubu 3 suka halarci taron. Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ita ce hukumar koli ta mulkin kasar Sin.

A wannan rana, a madadin majalisar gudanarwar kasar Sin, firaministan kasar Wen Jiabao ya gabatar da rahoton gwamnati mai ci a gun taron, inda ya bayyana ayyukan da gwamnatin ta yi cikin shekaru 5 da suka wuce. A cewar sa, shekaru 5 da suka gabatar shekaru ne masu ma'ana ga kasar Sin, gwamnatin kasar Sin ta cimma nasarar tinkarar rikicin hada-hadar kudi na duniya, da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, kana rayuwar jama'a da ayyukan bada tabbaci ga jama'a sun samu babban ci gaba.

Ban da gabatar da nasarorin da aka samu a shekaru 5 da suka wuce, Wen Jiabao ya bayyana matsalolin da kasar Sin ke fuskanta yayin da ake raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma, ciki hadda matsaloli da dama na raya tattalin arziki tare da kiyeye muhalli, haka nan akwai gibi babba a tsakanin yankuna daban daban a fannin samun bunkasuwa.

Wen Jiabao ya kara da cewa a kwai tazara tsakanin jama'a a fannin rarraba kudin shiga, tare da karin matsaloli a zamantakewar al'ummar kasar a fannonin bada ilmi, da samar da aikin yi, bada tabbaci ga jama'a, kiwon lafiya, samar da gidajen kwana, kiyaye muhalli, tabbatar da ingancin abinci da magani, kiyaye kwanciyar hankali a fannin sarrafa kayayyaki da zaman al'umma da dai sauransu. Shugaba Wen Jiabao ya kuma tabo batun da ya shafi yaki da cin hanci da rashawa a wasu sassa.

A cikin rahoton, Wen Jiabao ya sanar da burin kasar a bana a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, inda yace yawan kudin da aka samu daga sarrafar dukiyar kasar wato GDP zai karu da kashi 7.5 cikin kashi dari, za kuma a daidaita matsaloli da aka samu yayin da ake raya tattalin arziki, yawan farashin kayayyakin da jama'a suke saya zai karu da kashi 3.5 cikin kashi dari, kudin shiga na kowane mutum a kasar zai karu, tare da karin bunkasuwar tattalin arzikin kasar da dai sauransu.

Bisa tsarin taron za a kwashe kwanaki 12 ana gudanar da shi, za kuma a yi nazari tare da yanke shawara kan rahoton gwamnatin kasar, kana za a zabi sabbin ministoci da shugabannin hukumomin kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China