in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi nisa ga shirye-shiryen taron BRICS
2013-03-05 10:24:59 cri

Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta bayyana a ranar Litinin cewa, shirye-shiryen taro karo na biyar na kungiyar BRICS sun kama hanya sosai.

"A halin da ake, mun yi nisa ga shirye-shiryen dandalin BRICS karo na biyar. Kuma mun gamsu da matsayin shirye-shiryen da aka gudanar ta fuskar kayayyaki da gine-gine." in ji Ebrahim Ebrahim, sakataren kasa kan harkokin dangantakar kasa da kasa. Jami'in ya jaddada cewa. gwamnatin Afrika ta Kudu ta yi imanin cewa, wannan taro zai kasancewa nasara.

Taron BRICS karo na biyar zai gudana daga ranar 26 zuwa 27 na watan Maris a Durban, birnin tashar ruwa dake kudu maso yammacin kasar bisa taken "kasashen BRICS da Afrika, dangantakar samun bunkasuwa, dunkulewa da cigaban masana'antu". A karon farko ne kasar Afrika ta Kudu za ta karbi bakuncin babban taron BRICS, tun bayan da kasar ta samu shiga wannan kungiya a ranar 24 ga watan Disamban shekarar 2010 bisa goron gayyatar sauran kasashen da suka hada wannan gungu da ake kira BRICS.

Kungiyar BRICS, da kalmar ta kunshi harafin farko na kasar Brazil, Rasha, Indiya, Sin da kuma Afrika ta Kudu, ta hada kasashe masu tasowa dake samun cigaban tattalin arziki a duniya, haka kuma wadannan kasashe na rike da jimillar kudin ajiya na dalar Amurka biliyan 4500. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China