in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin
2013-03-05 09:30:47 cri

A ranar 5 ga wata da safe ne aka bude taron farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, inda Hu Jintao, da Xi Jinping da sauran shugabannin kasar Sin, da kuma wakilan jama'ar kasar kimanin dubu 3 suka halarci taron, wannan ya bayyana cewa, sabbin wakilan jama'ar sun fara aiki a hukunce.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan da aka fara aiwatar da manufar zabar wakilan jama'a da yawansu ya yi daidai tsakanin birane da kauyuka, yawan wakilan ma'aikata da manoma a wannan karo ya karu sosai, kuma yawan wakilan shugabannin jam'iyya da gwamnatin kasar ya ragu sosai, wanda hakan ke nuna kyautatuwar tsarin zabar wakilan jama'ar kasar Sin.

Wannan taron dake gudana a yanzu shi ne taron farko da sabbin wakilan jama'ar kasar Sin suka halarta.

Bisa tsarin taron za a kwashe kwanaki 12 ana gudanar da shi, za a kuma yi nazari kan rahoton gwamnatin kasar, kana wakilan jama'ar kasar za su yi nazari kan shirin gyara hukumomin gwamnatin kasar, da kuma ayyukansu, kuma za su tsaida shirin kwaskwarima a zagaye na biyu na kasar Sin. Ban da wannan kuma, yayin taron za a zabi sabbin ministoci da shugabannin hukumomin kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China