Yayin da Fu Ying ke zantawa da manema labarun, ta bayyana cewa, game da tsokanar da wasu kasashe suke yi, don gane da rikicin yankunan kasar, kamata ya yi Sin ta daidaita tare da magance rikicin cikin hanzari.
Da take amsa tambayar ko kasar Sin za ta dauki kwararan matakai don daidaita batutuwa da kasashen waje, Fu Ying ta bayyana cewa, kasar Sin ta sha bamban da manyan kasashen duniya, kuma tana da tsarin siyasa na daban, tare da tarin yawan al'umma, da samun saurin karuwar tattalin arziki, kuma har yanzu, tana ci gaba da saurin bunkasuwa, sabo da haka, wanda hakan ne ya sa wasu mutane ba sa fahimta kasar Sin sosai, haka kuma, akwai wasu mutane dake ci gaba da hasashen makomar kasar Sin bisa dangantakar kasa da kasa cikin shekaru 500 da suka gabata, wato idan kasar ta samu karfi, tabbas ne za ta ci gaba da daukar tsattsauran matakai, haka kuma, masu irin wannan tunani na gaggauta lalubo shaidun tabbatar da wannan zato nasu.(Bako)