Wannan kuma shi ne taron shekara-shekara na farko da 'yan majalisar ta CPPCC karo na 12 ke halarta, a cikin wa'adin aikinsu na shekaru biyar masu zuwa. Shugabannin kasar Sin Hu Jintao da Xi Jinping da sauran jagorori na halartar wannan biki na kaddamar da taron.
A madadin mambobin zaunannen kwamiti na majalisar CPPCC na karon da ya gabata, Jia Qinglin, shugaban majalisar karo na 11, ya gabatar da rahoton aiki na shekaru biyar da suka wuce, kana da bayar da shawarwari kan aikin majalisar na nan gaba.
Sabbin 'yan majalisar fiye da 2200 sun fara aikinsu daga yau, cikin su akwai 'yan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kimanin kashi 39.9 cikin dari, sanan nan yawan wadanda ba sa cikin jam'iyyar ba, ya kai kashi 60.1 cikin dari. A cikin kwanaki 9 masu zuwa, ake sa ran za su zabi shugaban sabuwar majalisar ta CPPCC da mataimakinsa, kana za su tattauna da kuma bayar da shawarwari kan muhimman manufofin kasar Sin da suka shafi siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewar al'umma da dai sauransu.(Kande Gao)