Wadannan manema labaru da suka fito daga kasashen ketare wasunsu suna aiki a wasu muhimman kafofin yada labaru na kasashe masu sukuni, wasu kuma sun fito daga kafofin yada labaru na kasashen Afirka da Latin Amurka da sauran kasashe masu tasowa. Batutuwan da suke jawo hankalinsu su ne manufofin tattalin arzikin kasar Sin, yanayin tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba, yiwuwar da ke akwai ga kasar Sin na aiwatar da sabuwar manufar sa kaimi kan bunkasar tattalin arziki, matakan da Sin za ta dauka wajen taimakawa warware rikicin basusukan Turai da dai sauransu. Ban da wannan kuma, kafofin yada labaru na kasashen ketare sun fi mai da hankali kan yadda kasar Sin za ta kyautata zaman rayuwar fararen hula, kamar ba da tabbacin zaman rayuwa, yin kwaskwarima kan aikin jinya da tsarin ba da ilmi da kuma daidaita farashin gidaje a kasuwar kadarori da dai sauransu.(Tasallah)