in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labarun Sin da na kasashen waje na mayar da hankali kan manyan taruka biyu dake tafe
2013-02-27 17:35:48 cri






Manyan tarurrukan majalissu guda biyu na kasar Sin, wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar, da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin, wadanda ake gudanarwa a kowace shekara, sun kasance muhimman batutuwan da suka shafi jama'ar kasar Sin ta fannonin siyasa da zaman rayuwa. Su ne kuma kafar dake bude ga kafafen watsa labaru na Sin da ma na kasashen waje, domin fahimtar yadda al'ummar kasar Sin suke a fagen neman bunkasuwa, da kuma muhimman manufofin da kasar za ta kaddamar nan ba da dadewa ba.

Shekarar 2013 shekara ce da za a samu sauyin jagorancin mahukunta a kasar Sin, wanda hakan ya sanya tarurrukan biyu na wannan shekara kara zamowa masu jawo hankulan kafofin watsa labaru na duniya baki daya.

Shekarar 2013 shekara ce da za a samu manyan sauye-sauye a kasar Sin, inda za a zabi sabbin shugabanni na gwamnati, ban da wannan kuma kasar Sin na cikin wani lokaci na gudanar sauyin tsarin tattalin arziki, da yin gyare-gyare kan hukumomin gwamnati, da tsarin raba kudin shigada jama'ar kasar suka samu. Hakan ya sa duniya zura ido kan manyan manufofin da sabuwar gwamnatin kasar ta Sin za ta kaddamar, domin amfani wajen farfado da tattalin arzikin duniya a dukkan fannoni.

Yayin da yake hira da wakilinmu, daraktan sashen Sinanci na kafar watsa labarai ta BBC , mista Li Wen ya bayyana cewa, kafarsu na mayar da hankali kan sabbin shugabannin kasar Sin da za a zaba, saboda wannan zai kawo tasiri ga tsarin gudanarwar harkokin kasar ta Sin a nan gaba, inda za a iya gano makomar bunkasuwar kasar ta Sin.

"Canjin manyan shugabannin gwamnatin Sin zai kawo tasiri ga manufar da kasar za ta bi, kan gudanar da harkokin diplomasiyya. Yanzu kasar Sin na kara taka rawa a duniya, wanda hakan ko shakka babu ya sanya kasashen duniya, kulawa da dukkan matakan da Sin za ta dauka a dandalin kasashen duniya."

Bayan haka Li Wen ya bayyana cewa, tun bayan da sabbin shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suka soma aiki a karkashin jagorancin Xi Jinping, matakan da suka dauka ta fuskokin hana cin hanci da rashawa, da gudanar da harkokin kasar bisa doka, da kuma inganta adalcin a fannin shari'a, da dai sauran muhimman fannoni, sun dauki hankalin kafofin watsa labaru na kasashen waje.

Saboda haka, batu kan ko sabuwar gwamnatin kasar za ta kara daukar matakai a wadannan fannoni yayin tarurrukan biyu dake tafe, shi ma ya jawo hankalin kafar ta BBC.

Ban da batutuwa game da siyasa, kafar ta BBC kuma, na kulawa da batun kiyaye muhalli sosai. Li ya ce,

"Mun maida hankali kan matsalar da kasar Sin ke fuskanta wajen kiyaye muhalli, ciki hadda gurbacewar iska da ingancin kasa. Saboda matsalar gurbatar muhalli, ba kawai tana kawo illa ga kasar ta Sin ba ne kawai, hakan na iya shafar ragowar yankunan duniya. Saboda haka, ana kulawa da matakan da gwamnatin kasar Sin za ta dauka wajen kyautata muhalli, da kuma irin nasarorin da za a cimma."

Batun kiyaye muhalli, shi ma ya kasance muhimmin batu da kafofin watsa labaru na yankin Hongkong na kasar Sin, za su zura ido a kai. Mataimakin babban edita a jaridar Wen Hui Pao ta Hongkong, Yin Shuguang, ya bayyana cewa, ko da yake kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen tattalin arziki a cikin shekaru sama da 30, tare da yin gyare-gyare, da bude kofa ga kasashen waje, duk da haka matsalar gurbacewar muhalli na kasancewa matsalar dake bukatar kulawar gaggawa da kasar ke fuskanta. Saboda haka, jaridar Wen Hui Pao, za ta mai da hankali kan batutuwan kara kiyaye muhalli, da kyautata yanayin muhallin, yayin da take watsa labaru game da tarurrukan biyu. Yin ya ce,

"Yanzu ba kawai ana bukatar bunkasa GDP, wato yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa ba ne kawai, a lokaci guda ana bukatar kiyaye muhalli, da tsimin makamashi.

Bugu da kari ana kokarin kara raya biraneda garuruwa a yankunan dake yammaci maso tsakiyar kasar Sin. Yanzu ana fuskantar matsalar gurbatar muhalli mai tsanani a gabashin yankunan kasar, don haka bai kamata ba a dauki yammaci maso tsakiyar kasar, ya zama irin na gabashin kasar."

Batun tattalin arziki shi ma ya zama muhimmin lamarin dake jawo hankulan kafofin watsa labaru, musamman ma a wannan matsanancin yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki. A matsayinta na kasa ta biyu wajen karfin tattalin arziki a duniya, ko sauyin tsarin tattalin arziki da kasar Sin za ta yi, da manufar bunkasuwar tattalin arziki da za ta bi a nan gaba za su iya kawo farfadowar tattalin arzikin duniya ko a'a? wannan tambaya ma, na jawo hankulan kasashen duniya. Babban mai sharhi na gidan talibijin na PHTV dake Hongkong, Du Ping ya bayyana cewa, kafarsu za ta mai da hankali kan ganin yadda za a inganta bukatun gida, da kuma dakatar da dogaro ga tsohuwar hanyar bunkasar tattalin arziki, da hada-hadar cinikayya ta fidda kayayyaki zuwa ketare a yayin tarurrukan biyu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China