in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Najeriya na kara hadin-gwiwa ta fuskar bunkasa al'adu
2013-02-26 15:37:27 cri






A ranar Litinin 25 ga wata ne wata tawagar jami'an kula da harkokin al'adu ta birnin Nanjing, na lardin Jiangsu dake kasar Sin ta kai ziyara birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriya, inda suka yi shawarwari da takwarorinsu na Najeriya, tare da rattaba hannu kan wasu takardun bunkasa fahimar juna a fannin al'adu.

Ministan al'adu, da yawon shakatawa, da kuma gyara halayen 'yan kasa na Najeriya, Mista Edem Duke, da jami'in kula da harkokin al'adu na ofishin jakadancin Sin dake Najeriyar Mista Jin Hongyue sun halarci taron shawarwarin.

A cikin jawabin da yayi, Mista Edem Duke ya yi maraba ga bakin na kasar Sin, sa'an nan yayi waiwaye kan hadin-gwiwa, da mu'amala dake wanzuwa ta fuskar al'adu, tsakanin kasashen Sin da Najeriya a wadannan shekaru. Ya ce, bayan da kasashen biyu suka cimma yarjejeniyar mu'amala da hadin-gwiwa a fannin al'adu, da ilmi a watan Maris din shekara ta 1990, ya zuwa yanzu, huldar al'adu tsakanin Sin da Najeriya na inganta kwarai da gaske.

A watan Mayun shekara ta 2012, an kafa cibiyar al'adu ta Najeriya a birnin Beijing, lamarin da ya sa Najeriya ta zama kasar Afirka ta farko wadda ta kafa cibiyar al'adunta a kasar China. Har wa yau kuma, wasu matasan Najeriya sun ziyarci kasar Sin, don koyon fasahar lankwasa jiki wato "acrobatics" a turance. Bayan da suka koma Najeriya, irin wasannin da suke yi sun samu babban yabo daga mataimakin shugaban kasar.

A watan Disambar shekara ta 2012 kuma, an yi bikin makon al'adun Najeriya a birnin Beijing, lamarin da ya kara inganta hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin kasashen biyu a fannin al'adu.

Mista Duke ya kuma bayyana muhimmancin al'adu, inda ya ce: "A ganina, al'adu na da muhimmancin gaske ga ci gaban tattalin arziki, siyasa, da kuma zamantakewar al'umma. Wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri a 'yan shekarun nan shi ne raya al'adu. Al'adu tamkar tushe ne na tattalin arziki, kuma al'ummar kasar Sin sun fahimtar hakan matuka. Idan Najeriya tana so ta cimma burin zama daya daga cikin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya nan shekara ta 2020, ya zama dole ta mayar da hankali kan muhimmiyar rawar da al'adu ke takawa."

Bugu da kari kuma, Mista Duke ya ce, a shekara mai kamawa wato shekara ta 2014, za'a yi gagarumin bikin cika shekaru dari da kafuwar Najeriya, kuma ya gayyaci gwamnatin kasar Sin don ta shirya shagalin "shekarar al'adun Sin" a Najeriya.

Shi ma a nashi jawabi, babban jami'in kula da harkokin al'adu na ofishin jakadancin Sin dake Najeriya Mista Jin Hongyue cewa yayi, mu'amala da hadin-gwiwar da ake yi a fannin al'adu tsakanin Sin da Najeriya suna shafar fannoni da dama, wato ba ma kawai irin mu'amalar da ake yi tsakanin masu ayyukan fasaha ba, lamarin ya kai ga kasar Sin ta fara fitar da kayan al'adunta zuwa Najeriya. Alal misali, a wajen bikin baje-kolin kayan fasaha da na al'adu na Afirka, wanda za'a yi a watan Yunin shekarar da muke ciki a birnin Abuja, za a ga kayayyakin kasar Sin.

Game da goron gayyatar da Mista Edem Duke ya ba shi kuwa, na shirya shagalin "shekarar al'adun Sin" a shekara ta 2014, Mista Jin Hongyue ya bayyana cewa:"Za mu ci gaba da zurfafa shawarwari tare da gwamnatin Najeriya, don shirya shagulgulan al'adu masu kayatarwa tsakanin Sin da Najeriya, ta yadda jama'ar kasashen biyu za su kara samun fahimtar juna, kuma zumunta dake tsakaninmu ta ci gaba da inganta."

Yayin shawarwarin da aka yi, shugaban babban dakin adana littattafai na birnin Nanjing na kasar Sin, ya bada kyautar littattafai guda 250 ga babban dakin adana liattattafai na Najeriya, wato "National Library of Nigeria", inda shugaban dakin malam Habib Abba Jato, ya nuna matukar godiya ga al'ummar kasar Sin:Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da muhimmanci, gami da babbar ma'anar yin hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin Sin da Najeriya ta fuskar al'adu, shugaban kwamitin kula da dakunan adana kayan tarihi, da kuma abubuwan tarihi da aka gada daga kaka da kakanni na Najeriya, wato "National Commission for Museums and Monuments", malam Yusuf Abdallah Usman cewa yayi: Bayan shawarwarin da aka yi, jami'ai masu kula da harkokin al'adu na kasar Sin da Najeriya, sun rattaba hannu a kan wasu takardun fahimtar juna uku, wadanda suka jibanci dakunan ajiye littattafai, da dakunan adana kayan tarihi, da kuma aikin kiyaye abubuwan tarihin da aka gada daga kaka da kakanni.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China