in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da daukar matakai don inganta aikin jinya ga manoma
2013-02-22 17:49:57 cri
Yanzu, manoma a kasar Sin da yawansu ya kai miliyan 800 a kauyuka na more sabon tsarin ba da aikin jinya cikin hadin gwiwa. A ranar 21 ga wata, bisa labarin da wakilinmu ya samu daga ma'aikatar kula da kiwon lafiya ta Sin, an ce, bayan da aka ci gaba da aiwatar da sabon tsarin ba da aikin jinya cikin hadin gwiwa a kauyuka, yanzu, yawan kudaden da manoma suke kashewa wajen jinya ya ragu.

Yayin taron da aka shirya a wannan rana, ministan kiwon lafiya na kasar Sin Chen Zhu, ya bayyana cewa, yawan kason kudin tallafi da gwamnatin za ta biya zai karu don rage yawan kudaden da manoma suke kashewa wajen kwanta jinya a asibiti zuwa kashi 60 cikin 100, don dai tabbatar da hakkin manoman.

Sabon tsarin ba da aikin jinya cikin hadin gwiwa a kauyuka ya kasance wani tsarin asusu da gwamnati, da manoma, da kungiyar manoma suka tattara kudi don kafa shi, domin idan manoma suka yi jinya, za su samu kudin tallafi daga cikin gudummawarsu, don rage musu wahala wajen biya kudade. Tun daga shekarar 2003, aka fara gwajin wannan tsari kuma, ya zuwa shekarar 2008, an cimma burin kafa wannan tsari a sassa daban daban na kasar Sin, kuma kafuwarsa ya kyautata rayuwar manoma da dama wadanda a baya jinya ke gagararsu.

A ranar 21 ga wata, ministan harkokin kiwon lafiya na kasar Sin Chen Zhu ya bayyana cewa, bayan karfafa wannan tsari, yawan kudaden da ko wane mutum ya tara cikinsa ya karu daga kudin Sin talatin zuwa dari 3 a shekarar 2012, kuma yawan kudaden tallafi da za a baiwa manoma da suka yi jinya a asibiti ya karu zuwa kashi 75 cikin 100, kana yawan kudaden tallafi da za a samar wa ko wane manomi ya wuce dubu 60. Chen Zhu ya ce, "Da farkon watanni 9 na shekarar 2012, mutane kimanin biliyan 1.15 ne suka mori sabon tsarin ba da aikin jinya cikin hadin gwiwa a kauyuka, kuma yawan kudaden da manoma suka biya wajen jinya da sayen magunguna ya ci gaba da samu raguwa, ya zuwa karshen watan Disamba, masu kamuwa da cututtuka da yawansu ya kai dubu 990 sun samu kudin tallafi ta wannan tsarin, ciki hadda wadanda suka kamu da manyan cututtuka, wanda hakan ya ceci iyalai da dama."

Huang Fanv wata mace da take zaune a gundumar Gan da ke lardin Jiangxi a kasar ta Sin, wadda ta kamu da cutar koda mai tsanani, sabo da haka, a ko wace shekara, ta kan kashe kudaden da yawansu ya kai kudin Sin Yuan dubun 50 zuwa 60 wajen jinya, a karshe dai, kudadenta suka kare. Daga nan sai ta fara yin aron kudi don yin aikin jinya, har wani lokaci ma, ta rasa abin da za ta yi, tun tana jurewa, har ta kai ta gaza, sabo da tsananin bukatar aikin jinya, ta ce, "Mun gamu da wahala sosai, idan a wannan mako, na je asibiti, sai kuma mako mai zuwa, ban san ina ne za je samun kudi ba? Gaskiya, na sha wahala, idan dangi suka gan ni na zo, sai su yi zaton, na sake zuwa don aron kudi daga wajensu ne."

A matsayinsa na wani wurin da aka yi gwajin wannan tsarin ba da aikin jinya cikin hadin gwiwa a kauyuka, daga shekarar 2011, lardin Jiangxi ya fara cin gajiyar aikin jinya game da tiyatar tace jini ga wadanda suka kamu da cutar koda a fayu, sabo da haka, Madam Huang ta samu saukin wahalarta sosai, shugaban asibitin cibiyar Nantang da ke gundumar Gan Likita Liu ya bayyana cewa, "Ana kashe kudaden da yawansu ya kai Yuan 320 a ko wane karo, kuma ana bukatar aikin jinya sau biyu a ko wane mako, wato kamata ya yi a yi tiyata har sau 104 a ko wace shekara, gaba daya, ta hanyar amfani da wannan tsari, ana tsimin kudaden da yawansu ya kai sama da dubu 30 a ko wace shekara, kuma tsarin ba da aikin jinya ya biya kudaden da yawansu ya kai kashi 70 cikin 100 daga cikin kudaden da manoman suke kashewa, sa'an nan kuma ma'aikatar kula da harkokin cikin gida su ma za su biya kudin tallafi da yawansu ya kai kashi 20 cikin 100, dadin dadawa kuma, hukumomin aikin jinya su ma, za su iya rage kashi 10 cikin 100 na kudin aikin jinyar." (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China