Kungiyar masu sarrafa albarkatun man fetur ta Afirka (APPA) ce zata shirya taron tare da hadin gwiwar ma'aikatar albarkatun man fetur ta Gabon, inji sanarwar da masu shirya taron suka bayar ranar alhamis din nan.
Babban taron na CAPE V zai kunshi zaman tattaunawa na tsawon kwanaki uku sannan za'a baje koli don nune-nunen kayayyakin albarkatun man fetur da kuma rangadin wasu ayyuka a wannan fanni inji sanarwar.
Taron har ila yau zai samu zuwan jiga jigan wakilai daga sassa na gwamnati da masu zaman kansu daga kasashe wadanda mambobi ne na kungiyar ta APPA da suka kunshi kasashen Aljeriya, Angola, Benin, Kamaru, jamhuriyar Congo, kwadibwa, Jamhuriyar dumokradiyar Congo, Masar, Equitorial Guinea, Gabon, Ghana, Libya, Mauritania, Nijar, Najeriya, Afirka ta Kudu, Sudan da Chadi.
Bugu da kari taron zai samu halartar wakilai daga cibiyoyin kasa da kasa, kamfanonin man fetur, da dai sauran kamfanoni masu harkar man fetur daga nahiyar Afirka.
Sanarwar ta ci gaba da cewa wannan babban taro zai samar da wata muhimmiyar dama, wacce ita ce irinta na farko, ga masu harkar man fetur wadanda suka samu kafuwa da ma wadanda ke neman su fara harka a Afirka. (Lami Ali Mohammed)