Najeriya ce ta zamo zakarar kwallon kafar nahiyar Afirka ta bana, bayan da ta lashe wasan karshe da ya gudana tsakanin ta da Burkina Faso a jiya Lahadi 10 ga watan nan. Wasan wanda aka buga a filin wasa na Soccer City, an tashi ne Najeriya nada ci 1 yayin da ita kuma Burkina Faso ke nema.
Wannan nasara ta kawo karshen dogon jiran da Super Eagles tasha n tsawon shekaru 19, tun bayan daukar wannan kofi da tayi a shekara ta 1994.
Dan wasan Najeriya Sunday Mba ne dai ya ciwa Super Eagles din wannan kwallo guda 1, cikin kimanin mintuna 40 da fara wasan, bayan da Victor Moses ya shararo kwallo harabar da'irar mai tsaron gidan Burkina Faso.
Wannan kwallo da Mba dan shekaru 24 da haihuwa, wanda kuma ke bugawa kungiyar Warri Wolves kwallo a gida Najeriya,ta jefa farin ciki a zukatan dubban 'yan kallo, dama miliyoyin 'yan Najeriya dake fadin duniya, ta kuma kawo karshen dukkanin wani ragowar hasashe da aka yiwa wannan gasa a baya. Dama dai wannan dan wasa shine ya ciwa Najeriya kwallon ta ta 2, yayin wasan da ta yi da kasar Ivory Coast ranar Lahadin da ta gabata, wanda kuma aka tashi ci 2 da 1.
Yan wasan Super Eagles dai sun ta kai hare-hare kafin tashi daga wasan, duk da dai cewa basu samu nasarar kara kwallo bayan wannan guda daya da Mba ya zura ba.
Suma 'yan wasan Burkina Faso, wadanda suka ciwa wannan gasa alwashi, sun yi iyakacin kokarin su, domin rama wannan kwallo da ta makale musu, amma hakan yaci tura, musamman ganin yadda 'yan wasan Najeriya irin su John Obi Mikel, da Elderson Echiejile, da Efe Ambrose, dama Kenneth Omeruo suka yi bangabanga, tare da tare dukkanin wani farmaki da ka iya sanadiyar farke waccan kwallo.
Duk da hakan, dan wasan Burkina Faso Prejuce Nakoulma, ya samu damar kai wani mummunan hari ciki minti na 73 da fara wasan, kwallon da mai tsaron gidan Najeriya Vincent Enyeama ya hana ta shiga raga.
Tarihin wannan gasa dai ya nuna cewa Kocin Super Eagles Stephen Keshi ne na 2, cikin 'yan wasan Afirka da suka taba daukar wannan kofi yana dan wasa, sa'an nan kuma ya dauka yana koci, baya ga takwaran sa Mahmoud El Gohary, wanda shima ya bugawa kasar Masar wannan gasa a shekarar 1959, lokacin da ta dauki kofin, ya kuma sake daukar kofin lokacin yana kocin kungiyar ta Masar a shekarar 1998.
Kofin da Najeriya ta dauka a bana shine na 3 gare ta, kuma na farko da Keshi ya samu nasarar dauka a matsayin kocin kungiyar.
Kuma idan dai ba a manta ba, keshi shine kaftin din Super Eagles din a shekarar 1994, lokacin da suka dauki kofin na wannan shekara.
Wannan nasara da Najeriya ta samu, za ta bata damar shiga gasar cin kofin zakarun nahiyoyi, wanda da za a yi cikin watan Yuni mai zuwa a Brazil, inda zasu kara da ragowar zakaru kamar Tahiti, da Uruguay, da kuma Spain, a gasar da za ta zamo tamkar share fage ne ga gasar cin kofin duniya dake tafe.
A bangaren kasar Burkina Faso data zo ta biyu a wannan gasa ta bana kuwa, da dama daga manazarta harkokin kwallon kafa na ganin matakin na 2 gare su babbar nasara ce, ganin wannan ne karon farko da suka kaiga hakan.
Tuni ma Kocin ta Paul Put, ya jinjinawa kwazon 'yan wasan sa,yana mai cewa ya gamsu da yadda suka dage ganin sun samu nasara a wasan tun daga farkon sa har karshe, acewar sa hakan abin a yaba ne.
Put, ya lasafta nasarar fidda Zambia da Ghana da suka yi a baya, a matsayin abin a yaba da 'yan wasan nasa suka yi.
Kamar dai yadda akan ce "A sha ruwa a koma wasa" A yanzu dai kasar Burkina Faso za ta shiga wasannin ta na share fagen gasar cin kofin duniya nan da makwanni 6 masu zuwa, inda za ta buga wasa da kasar Niger a birnin Wuagadougou.