in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi masana'antun Sin su dauki alhakin tsimin makamashi da rage yawan hayaki mai gurbata muhalli
2013-02-08 17:46:07 cri
Kwanan baya, yanayin hazo da kasar Sin ta gamu da shi, ya kawo babbar illa ga lafiyar jama'a, wanda hakan ya jawo hankalin jama'a wajen inganta kiyaye muhalli da tsimin makamashi, gami da rage yawan hayaki mai gurbata muhalli.

Bisa sakamakon nazari da aka yi, an ce, yawan hayaki da masana'antu suke fitarwa shi ne ya sabbaba gurbatar muhalli a kasar Sin. Don rage yawan abubuwa masu gurbata muhalli da masana'antun suke fitarwa. Yanzu, hukumomin kiyaye muhalli da masana'antun da abin ya shafa, suna tashi tsaye, don lalubo bakin zaren tsimin makamashin da rage yawan hayaki mai gurbata muhalli.

Kamfanin samar da wuta, da iska mai dumi na Hanglian, wani kamfani ne da ke da manyan na'urorin zamani, a yankin raya tattalin arziki da fasahohi na birnin Hangzhou, a lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, wanda ke daukar nauyin samar da wuta da iska mai dumi ga dakunan asibitoci da makarantu, da masana'antu sama da 10 a wurin. A dakin gudanar da aiki, wani ma'aikaci mai suna Zhang Yumin, ya fada wa wakilinmu cewa, babban aikinsa shi ne a lura da sauyarwar kididdigar da ake samu game da yawan hayaki mai gurbata muhalli da ke cikin na'urar, idan aka gano, yawan hayaki mai gurbata muhalli ya karu, zai dauki matakai don shawo kan lamarin. Ya ce, "Za a kara wani sinadari a ciki, don rage yawan hayaki na "sulfur dioxide" da zai fita, haka kuma idan aka kara yawan ruwan ammonia, za a rage yawan hayakin nitrogen oxide da za a fitar."

Hayakin "sulfur dioxide" da "nitrogen oxide", muhimmin hayaki mai gurbata muhalli da kamfanin samar da wuta da iska mai dumi ke fitarwa, kuma wadannan hayaki mai gurbata muhalli yana da alaka sosai da muhallin iska, kuma su ne suke kawo muhimman abubuwa masu gurbata muhalli na PM 2.5. Bayan da aka samu yanayin hazo a kasar Sin, gwamnatoci na wurare daban daban sun fara daukar matakai wajen sa ido game da adadin PM 2.5.

Haka kuma, yawan kwal da ake yin amfani da Shi a kasar Sin ya kai kashi 70 bisa 100 cikin dukkan makamashin da ake amfani da su, yadda za a amfani da kwal cikin inganci ba tare da gurbata muhalli ba, ya zama wata babbar matsala ga masana'antu masu samar da wutar lantarki. Haka kuma, yanzu, bayan da kamfanin Hanglian ya yi gyare-gyare game da fasahohinsa, ya riga ya saka jari da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 60 wajen rage yawan hayakin sulfur dioxide da nitrogen oxide da ke fitarwa sakamakon amfani da makamashin kwal, sannan kashi 70 bisa 100 daga cikinsu gwamnanti ce ta bayar a matsayin kudin taimako.

Manajan kamfanin Hanglian Min Wei ya bayyana cewa, bayan da kamfaninsa ya yi gyare-gyare, fasahar kamfanin wajen kiyaye muhalli tana sahun gaba a duniya. A ko wace shekara, ana iya rage yawan kwal da ya yi amfani da shi da Ton 6 zuwa 7, ta hakan ne, ana iya rage yawan hayaki na sulfur dioxide da nitrogen oxide da yawansu ya kai Ton sama da 1000, kuma yawan hayaki mai gurbata muhalli da ake iya janyewa ya karu daga kashi 99.3 zuwa kashi 99.9 Ya ce, "Bai kamata a raina wannan lissafi da bai kai kashi 1 cikin 100 ba, sabo da dukkansu, abubuwa ne masu gurbata muhalli."

A birnin Hangzhou, akwai masana'antun samar da wuta da iska mai dumi da yawansu ya kai kimanin 30. Bisa burin rage yawan hayaki mai gurbata muhalli da birnin Hangzhou ya tsara a cikin shiri na 12 na raya kasa cikin shekaru biyar-biyar masu zuwa, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2013, kamata ya yi duk wadannan masana'antu su yi gyare-gyare don rage yawan hayaki mai gurbata muhalli, nan da shekarar 2014, kamfanonin da ba za su kammala cikin gyare-gyare ba, za su fuskanci hukunci mai tsanani. "Mun bukaci dukkan kamfanonin da su kammala aikin rage yawan hayaki mai gurbata muhalli kafin shekarar 2013, idan ya zuwa shekarar 2014, ba a cimma wannan buri ba, za a hukunta su, tare da tilasta musu rufe kamfanonin. Yanzu, akwai manyan kamfanoni 5 na samar da wuta da iska mai dumi da suka kammala rage hayaki mai gurbata muhalli, sauran kananan kamfanonin da suka kammala wannan aiki sun kai sama da 10. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China