in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar musulmi ya yi kira da a warware rikicin kasar Sham ta hanyar yin shawarwari
2013-02-08 11:31:44 cri
An rufe taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar Musulmi na tsawon kwanaki biyu a birnin Alkahira, hedkwatar kasar Masar, inda mahalartan taron suka ba da takardar karshen taro, da yin kira ga bangarori daban-daban da rikicin kasar Sham ya shafa da su dakatar da nuna karfin tuwo tare kuma da warware rikicin ta hanyar yin shawarwari.

A gun bikin rufe taron, shugaban kasar Masar Mohammed Morsi ya nuna cewa, mahalarta taron su amince da ci gaba da yin amfani da rukunin shiga tsakani a rikicin kasar Sham da ta kunshi Iran, Masar, Saudiya da Turkiya, tare kuma da kalubalantar kungiyoyoin adawa da su yi shawarwari da gwamnati domin kawo karshen rikicin tun da wuri. A sa'i daya kuma, mahalartan sun nuna goyon baya ga aikin shiga tsakani da wakilin musamman na MDD da AL Lakhdar Brahimi ya yi kan rikicin kasar Sham cikin wannan takarda.

Yayin da aka tabo batun Palasdinu, mahalartan sun amince da baiwa Palasdinu tallafin kudi tare kuma da yin kira ga kasashen Larabawa da su dauki matakai da suka dace domin yaki da matakin da Isra'ila ta dauka na gina matsugunan Yahudawa.

Game da batun kasar Mali, wannan takarda ta nuna goyon baya ga ikon mulki da 'yancin kan kasar, kuma ta jaddada wajibcin baiwa kasar Mali tallafin kudi da kayayyaki. Shugaba Morsi ya ce, mahalartan sun amince da a kafa wata gwamnatin wucin gadi a Mali da kuma gudanar da zaben majalisar dokoki bisa daidaici da adalci tare kuma da goyon bayan kungiyar tarrayar kasashen Afrika wato AU da ta tura sojinta karkashin jagorancin kasashen Afrika zuwa Mali. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China