in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Masar ya yi kira ga kasashen Musulmi da su karfafa hadin gwiwa da amincewa juna tsakaninsu
2013-02-07 15:06:50 cri
Ran 6 ga wata, yayin bikin bude taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar mabiya addinin Musulunci karo na 12, da aka yi a birnin Alkahira, shugaban kasar Masar Mohamed Morsy ya bayyana cewa, a halin yanzu dai, kasashen Musulunci na fuskantar kalubale da dama, don haka, ya yi kira ga dukkan kasashen Musulmi wadanda mambobi ne na kungiyar da su karfafa hadin gwiwa da amincewa juna tsakaninsu.

Da farko dai, shugaba Mohamed Morsy ya nuna matukar godiya ga kasashen Musulmi dangane da taimako da kuma goyon baya da suka baiwa kasar Masar yayin da kasar take cikin yanayin tashin hankali, Ya kuma bayyana cewa, ko da yake kasashen Musulmi na da wadatattun albarkatan halitta, amma halin ci gaban kasashen bai iya biyan bukatun jama'a ba, kamar a fannoni na ci gaban kimiyya da fasaha, kudaden da aka zuba wajen raya ayyukan koyarwa, da kuma kiyaye muhalli da dai sauransu. Shi ya sa shugaba Mohamed Morsy ya yi kira ga dukkan kasashen mambobin kungiyar da su kara hadin gwiwa a wadannan fannoni ta yadda za a iya daga matsayin kungiyar hadin gwiwar masu bin addinin Musulunci a duniya.

Ya kuma ba da shawara cewa, ya kamata a kafa wani tsari mai amfani wajen yin shawarwari tsakanin mambobin kungiyar, don warware rikice-rikice da kuma kalubale da ke tsakanin kasashen Musulunci cikin lumana.

Yayin da yake magana kan yanayin kasar Syria, Mohamed Morsy ya sa kaimi ga dukkan kungiyoyin adawar kasar da su kara yin hadin gwiwa tsakanin su, sa'an nan ya sake jadadda cewa, kasar Masar ta ki yarda da shisshigin soja da za a yi ta kowace hanya.

Bugu da kari, cikin jawabinsa, Mohamed Morsy ya taya kasar Falesdinu murna kan nasarar da ta samu wajen zama mambar sa ido a MDD, inda ya kuma yi kira ga dukkan kasashen mambobin kungiyar da su nuna mata goyon baya don kafa wata kasar Palesdinu wadda birnin Jerusalem ta gabas ya zama hedkwatarta, kuma tana da ikon mallakar kanta da mulkin kai sosai. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China