Ecobank ya bude ofishi a birnin Beijing a watan Disamban shekarar 2012 kana yana da wata hadin gwiwa da Bankin China na kasar Sin.
Shugaban bankin na Ecobank a kasar Kenya Tony Okpanachi ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a birnin Nairobi cewa, ana cin gaba da samun bunkasar harkar cinikayya tsakanin 'yan kasuwa na Sin da Afirka inda hakan ya sa ake bukatar wata cibiyyar harkar kudade dake da rassa a kasashe da dama wacce za ta samar masu saukin gudanar da harkokin kudade.
Ya ce, ana samun ci gaban zuba jari daga kasar Sin a nahiyar Afirka a 'yan shekarun nan, kuma bisa dukkan alamu za a samu ci gaban hakan wanda shi ne ya sa bankin shi ma ke kara fadada ayyukansa don cin moriya a fuskar cinikayyan.
Kididdiga daga ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin na nunin cewa, Afirka za ta zarce kungiyar tarayyar Turai da kasar Amurka a matsayin babbar abokiyar harkar cinikayya nan da wani lokaci mai zuwa.
Sakamakon bunkasar harkar cinikayyan, ana sa ran cewa, za a samu karin gamayya tsakanin cibiyoyin harkokin kudi na kasashen Sin da Afirka, inda za su kara bunkasa hadin gwiwa tsakaninsu kamar wadda aka kulla a shekarar 2007 inda bankin masana'antu da cinikayya ICBC na kasar Sin ya sayi kashi 20 cikin dari na hannun jarin bankin Standard Bank dake Afirka ta Kudu.
Haka zalika, bankin Exim na kasar Sin shi ma yana cikin wadanda suka mallaki hannun jari na bankin harkokin shige da fice na kayayyaki na Afirka.
Bugu da kari, bankin kasar Sin shi ma ya bude ofisoshi a kasashen Afirka da dama da suka hada da kasar Kenya. (Lami)