Wasan ranar Lahadi 3 ga wata da Nigeria ta buga da Ivory Coast ya ba da mamaki, domin kuwa Najeriya ce ta samu nasarar lashe wasan da ci 2 da 1. Dan wasan Super Eagles Emmanuel Emenike, da Sunday Mba ne suka zira kwalakwale ga Nijeriya, yayin da Cheick Tiote ya jefawa Ivory Coast kwallonta daya tilo.
Tun da farko dai Emenike ne ya fara cin kwallo a minti na 42 da fara wasa, amma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci cikin minti na 49 Cheick Tiote, ya farke wannan kwallo, kuma bayan daukar dogon lokaci ana gumurzu, Sunday Mba na Super Eagles ya yi kukan kura ya jefawa super Eagles din kwallo ta biyu cikin minti na 77.
Haka kuma aka tashi wannan wasa inda Ivory Coast ta yi iyawarta ta farke amma hakan ya faskara, lamarin da ya sanya Najeriya matsawa ga wasan kusa da na karshe da za ta buga ranar Laraba da kasar Mali, yayin da ita kuma Ivory Coast wa'adin komawarta gida ya yi.
Dangane da sauye-sauyen 'yan wasa kuwa, kocin Super Eagles na Najeriya Stephen Keshi, ya sauya 'yan wasa biyu ne kawai, daga jerin 'yan wasan da suka bugawa Super Eagles din wasanta da Habasha, wato Fegor Ogude wanda Ogenyi Onazi ya canza, da kuma Aide Ideye wanda ya canji Ikechukwu Uche.
Shi kuwa a nasa bangare kocin Ivory Coast Sabri Lamouchi, dawo da 'yan wasansa kwararru ya yi a wannan karo, bayan wasu daga cikinsu sun huta, a wasansu da ya gabata da Algeria. 'Yan wasa irin su Yaya Toure, da Didier Drogba, sun sha kai farmaki don ganin sun karya lagon Najeriya amma hakan ya faskara
Yayin wannan wasa dai Victor Moses, da Emenike sun furnaci Ivory Coast matuka da gaske, su kuma 'yan wasan Ivory Coast irinsu Drogba, da Tiote, da kuma Salomon Kalou sun yi ta kai nasu hare-haren kafin kaiwa ga karshen wasan.
Sai kuma wasa na biyu tsakanin Burkina Faso da Togo wanda aka buga a filin wasa na Mbombela dake Rustenburg, wasan wanda shi ma ya kayatar matuka an tashi ne Burkina Faso na da ci 1, yayin da Togo ke nema.
Shahararren dan wasan kasar ta Burkina Faso Jonathan Pitroipa ne dai ya ci wa kasar tasa kwallo bayan an kai ruwa rana, an kuma shafe mintuna 90 babu ci. Amma cikin karin lokaci a minti na 104 sai Pitroipa ya samu damar sharara kwallo a ragar Togo, matakin da ya sanya a yanzu haka Togo ke adabo da wannan gasa, ita kuma Burkina Faso ke shirin fuskantar Ghana a wasan ta na daf dana karshe.
Daga bangaren Burkina Faso Jonathan Pitroipa, da Charles Kabore, da Nakoulma sun yi matukar kokari a wannan wasa, wanda wasu ke ganin dama su ne suka cancanci samun nasararsa. Kuma wannan ne karo na 2 da suka taba kaiwa ga wannan matsayin kasancewa cikin kasashe 4 na karshen gasar, kuma karon farko da suka samu wannan nasara a wajen kasarsu tun bayan shekarar 1998.
Suma 'yan wasan Togon kamar su Saidou Panandetiguiri, da Vincent Bossou, da Prince Segbefia, Dove Wome da Moustapha Salifou, sun yi iyakacin kokari yayin wannan wasa kafin dai a kai ga tashi bayan an sha su kwallo daya mai ban haushi.
Yanzu dai babu abin da ya rage illa mu sanya ido mu ga yadda wasan Najeriya da Mali, da kuma Burkina Faso da Ghana za su wakana a ranar Laraba 6 ga wata mai zuwa.