Sanarwar ta bayyana cewa, shugaban kasar Faransa Francois Hollande, tare da Madam Bokova sun kai ziyara a kasar Mali tare. Haka zalika sanarwar ta ce, daya daga dalilan ziyarar shi ne, kaddamar da aikin tantance yanayin da ake ciki a kasar ta Mali a fannin kiyaye kayayyakin tarihi, musamman bisa la'akari da yadda wutar yaki ke ruruwa a kasar, sa'an nan Madam Bokova za ta kaddamar da wani shiri tare da gwamnatin kasar, na wanzar da ayyukan hukumar ta UNESCO a Mali.
An ce, wannan ziyara za ta baiwa Madam Bokova damar tattaunawa da masu fada a ji na hukumomin Timbuktu da Bamako, kana za ta kaddamar da shirin kungiyarta na tallafawa don kare, da kuma sake gina kayayyakin tarihi na al'adu dake kasar ta Mali.
Yanzu dai kasar Malin na da manyan kayayyakin tarihi da al'adu 4, ciki hadda tsohon garin Timbuktu, da kabarin Askia dake garin Gao. (Bello Wang)