in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana da Mali sun samu nasarar shiga wasan kusa da na karshe na gasar kwallon kafa ta cin kofin Afirka
2013-02-03 14:57:33 cri






Yanzu dai mafarkin Cape Verde a gasar cin kofin kwalon kafar nahiyar Afirka da ke gudana a Afirka ta kudu ya kare, bayan da kasar Ghana ta llasata da ci 2 da nema, a wasan gab da kusa dana karshe da suka buga jiya, a filin wasa na Nelson Mandela Bay, abin da ya baiwa kasar Ghana damar kaiwa ga wasan kusa da na karshe, inda za ta kara da kasar da ta yi nasara a wasan da za a buga yau tsakanin Burkina faso da Togo.

Dan wasan Ghana Mubarak Wakaso ne ya fara zurawa Ghanan kwallo, a wani bugun da suka samu a wajen shatin mita 16, bayan da dan kasar Cape Verde ya aikata laifi. Kana a minti na 53 Ghana ta samu bugun daka kai sai mai tsaron gida, bayan da aka yiwa Asamaoh Gyan keta, amma saboda rashin sa'arsa ta bugu "penalty", sai aka baiwa Mubarak damar sake buga wannan kwallo, kuma ya zura ta a ragar 'yan kasar ta Cape Verde ba tare da wata matsala ba.

Koda ya ke suma 'yan Cape Verde sun yi ta kai hare-hare, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, haka dai aka tashi wasan Ghana nada ci 2, Cape Verde na nema, sakamakon da ya baiwa Ghana damar tsallakewa zuwa wasan kusa dana karshe a wannan gasa.

A wasa na biyu kuma tsakanin Afirka ta kudu mai masaukin baki da Mali, sai da wasan ya kai ga bugu daga kai sai mai tsaron gida, bayan da aka cika mintuna 120 cif ana ci 1 da 1.

Afirka ta kudu ce ta fara zura kwallo a minti na 32 kafin a tafi hutun rabin lokaci, ta hannun dan wasanta Tokelo Rantie, inda 'yan kallo kusan 50,000 ke zura ido, tare da zuga 'yan wasan na Bafana-Bafana.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci cikin mitinu 52, dan wasan Mali Seydou Keita ya farkewa kasarsa kwallon da 'yan wasan na Bafana-Bafana suka zura musu a mintuna na 23.

Haka dai a kai ta fafatawa har mituna 120, kafin daga bisasi a shiga bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Daga karshe dai Mali ta zura kwallaye 3 yayin da Afirka ta kudu ta ci kwallo daya tak cikin bugun daga kai sai mai tsari gida da suka yi.

A yau Lahadi kuma za a taka leda ne tsakanin Nigeria da Ivory Coast, sai kuma wasa na biyu tsakanin Togo da Burkina Faso.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China