in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta ci gaba da mai da hankali game da aikin gona a shekarar 2013
2013-02-01 18:21:55 cri
A ranar 31 ga watan Janairu na shekarar 2013, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta fitar da takarda ta farko ta shekarar 2013, inda ta sake mai da hankali sosai game da aikin gona, kauyuka da manoma, kuma wannan shi ne karo na 10 da Sin ta mai da hankali game da aikin gona cikin takardar farko cikin shekaru 10 da suka gabata a jere.

Manyan batutuwan da ke cikin wannan takarda mai muhimmanci ta farko da gwamnatin tsakiya ta fitar, su ne, yin gyare-gyare game da aikin gona, da raya aikin gona na zamani, da samun sabbin dabarun yin kasuwanci a fannin noma. Game da batutuwan da manoma suka dora muhimmanci sosai a kai, a cikin takardar, an mayar da martani a kansu. A ranar 1 ga watan Febrairu, a nan birnin Beijing, yayin da mataimakin shugaban rukunin kula da aikin gona na kwamitin tsakiya na kasar Sin Chen Xiwen ke zantawa da manema labaru na gida da waje, ya bayyana cewa, kamata ya yi a gaggauta raya aikin gona na zamani, kuma abubuwa masu muhimmanci dake kunshe a ciki su ne kara kuzari ga kauyuka, da karfafa zukatan manoma, don tabbatar da moriyarsu.

Takarda mai muhimmanci ta farko ta zamanto takarda ta farko da kwamitin tsakiya ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya fitar a ko wace shekara, wadda ke iya ba da jagoranci ga dukkan ayyukan kasar Sin za ta gudana a duk sabuwar shekara.

Takarda mai muhimmanci ta farko da aka fitar a bana, ta bayyana yadda za a raya aikin gona na zamani, da samun sabbin dabarun yin kasuwanci a fannin noma, game da wannan, mataimakin shugaban rukuni raya aikin kauyuka na gwamnatin tsakiya Chen Xiwen ya bayyana cewa, "Kamata ya yi a gaggauta raya aikin gona na zamani. Ban da samar da kudi, fasahohi, da kayayyaki da kuma na'urori, yanzu lokaci ya yi da za a yi kokarin samun sabbin dabarun yin kasuwanci a fannin noma, da kara kuzari ga kauyuka da karfafa zukatan manoma, ta yadda za a yi kokarin raya aikin gona cikin dogon lokaci."

A cikin shekaru 2 da suka gabata, aikin gona na kasar Sin ya samu bunkasuwa cikin gaggawa, cikinsu, yawan hatsin da aka samu a shekarar 2012 ya kai kilogram biliyan 590, kuma yawan hatsin da aka samu ya samu girbi cikin shekaru 9 a jere, haka kuma bisa yunkurin da ake yi na raya masana'antu da harkokin sadarwa, kana da karuwar garurruwa, an samu manyan canje-canje a kauyuka, haka kuma ana ta samun sabbin dabarun yin kasuwanci a fannin noma.

Amma, yayin da ake kokarin raya garurruwa, wasu matsaloli da dama sun kunno kai, bayan da matasa masu karfin jiki a jika da yawansu ya kai sama da miliyan 260 suka samu aikin yi a birane da garurruwa, kuma sun bar aikin gona a kauyuka, yanzu, ana fuskantar matsalar rashin 'yan kwadago a kauyuka, abin da ya haifar da babban kalubale game da aikin samar da isasshen abinci a kasar. Chen Xiwen ya bayyana cewa,

"Game da raya sabbin hanyoyin yin kasuwanci a fannin noma, ban da sa kaimi ga manoma da su inganta karfinsu, kamata ya yi gwamnatin ta sa kaimi da nuna goyon baya game da batun raya kungiyar hadin kan manoma ta sabon salo, hadin kan manoma wajen yin kasuwanci gama-gari da dai sauransu."

Haka kuma, Chen Xiwen ya ci gaba da bayyana cewa, kamata ya yi a sa kaimi ga masana'antu da 'yan kasuwa da su zuba jari a bangaren aikin gona, amma a sa'i daya kuma, ya jaddada cewa, yanzu, za a gabatar da tsarin samun iznin sa ido game da aikin gona, don tabbatar da moriyar manoma. Ya ce, "Ba za a yarda ba masana'antu da ke da jari da dama sun rika kwace hakkin yin kasuwanci ta fuskar noma daga manoma marasa galihu, kamata ya yi mu karfafa zukatan manoma da suke da niyyar gudanar da aikin gona a kauyuka su ci gaba da sana'o'insu."(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China