An fara gasar cin kofin kwallon kafan Afirka ce a birnin Khartoum na kasar Sudan a shekara ta 1963, kuma kasar Ghana wadda za mu fara bayani a kanta cikin wannan shirin, ta fara zuwa gasar ce a shekara ta 1963, lokacin da ta karbi bakuncin gasar kuma ta lashe kofin bayan da ta doke Sudan a wasan karshe.
Bayanai sun nuna cewa kasar ta Ghana ta dauki bakuncin wannan gasa ce sau 4, wato a shekara ta 1963, 1978 da 2000 lokacin da suka dauki bakuncin gasar tare da Najeriya da kuma wadda ta dauki bakunci a shekara ta 2008, ta kuma halarci gasar sau 19. Tana kuma rike da kofin dindindin na farko a wannan gasa, wanda aka bata a 1978 bayan ta lashe kofin sau 3.
Bisa jimilla Ghana ta dauki kofin sau 4, wato a shekara ta 1963 kamar yadda muka fada da farko da shekara ta 1965, 1978 da kuma 1982.
Ganin yadda Ghana ta dauki bakuncin wannan gasa mai muhimmanci da aka fara tun a shekara ta 1965, ta kuma lashe kofin har sau 4 a tarihi, ita kuma kasar Cape Verbe, wannan shi ne karo na farko da ta halarci gasar, don haka, wannan abin alfahari ne ga wannan karamar kasa da har ta kai ga wannan mataki a halin yanzu.
Sai kuma kasar Afirka ta kudu mai masaukin gasar a wannan karo, ta halarci gasar ne sau 8, ta kuma dauki bakuncin gasar ce a shekara ta 1996, kana ta lashe kofin a wannan lokaci. Kana ta zamo ta biyu sau 1 da na uku sau 1.
Yayin da sauran kasashe kamar Ghana da Kamaru suka lashe wannan kofi a lokuta dabam-dabam. Ita kuma Mali da a halin yanzu ta samu nasarar kaiwa ga zagaye na biyu na wannan gasa da ke gudana a kasar Afirka ta kudu a wannan karo, bayanai sun nuna cewa, ta halarci gasar ce ita ma sau 8, ta kuma dauki bakuncin gasar a shekara ta 2002, koda ya ke Kamaru ce ta lashe kofin a wasan karshe da suka yi da kasar Senegal, inda suka tashi ci 3 da 2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, yayin da kasar Mali mai masaukin gasar ta zo ta 4.
Yanzu kuma bari mu koma ga kasar Ivory Coast, wadda bisa tarihi ta dauki kofin nahiyar ta Afirka sau daya tak, wato a shekarar 1992, shekaru 21 ke nan da suka gabata, ta kuma zo na biyu sau 2, na uku sau 4 da kuma na hudu sau 2. Karfin da wannan kungiya a bana a fili yake ganin yadda manyan 'yan wasanta irin su Didier Drogba, Kolo Toure, Didier Zokora, Gevinho ke taka leda yadda ya kamata. Tana kuma daya daga kasashen da ake zatawa daukar kofin a bana.
Sai kuma Nigeria da ta yi hadin gwiwar daukar bakuncin wannan gasa da Ghana a shekara ta 2000, ta kuma dauki bakuncin gasar ita kadai a shekarar 1980. Nigeriar ta kuma lashe kofin sau 2, wato a shekarun 1980 da kuma 1994. Ta zo na biyu sau 4, da kuma na uku sau 7. Ita ma ta na cikin wadda 'yan wasanta suka dade ana damawa da su a wannan gasa. A bana ta zo da kwararrun 'yan wasa irin su mai tsaron gida Vincent Enyeama, Joseph Yobo, Efe Ambrose, Azubuike Egwuekwe, Ahmed Musa, Emmanuel Emenike, John Obi Mikel, Victor Moses, da dai sauran su.
Ita kuwa kasar Burkina Faso ta karbi bakuncin wannan gasa ce a shekarar 1998, shekarar da ta fi taka rawar gani ke nan, inda a wannan gasa ta zo ta 3. Sai kuma a bana da ta samu damar shiga zagaye na 2. Kamar dai ragowar kasashe da ke halartar wannan gasa a bana Burkina Faso ta zo da 'yan wasa irin su Bakary Koné, da Charles Kaboré, Alain Traoré, Jonathan Pitroipa, da kuma Abdou Razack Traoré.
Daga karshe akwai kasar Togo, wadda sabon shiga ce a wannan zagaye na biyu, na gasar cin kofin nahiyar Afirka. Ta kuma zo gasar ta bana da 'yan wasa irin su Floyd Ayite, Emmanuel Adebayor, da Gakpe.
Yanzu dai lokaci kawai za mu jira mu ga shin ko tsofaffin hannu irin su Ghana, Nigeria, Afirka ta Kudu, Mali da Ivory Coast ne za su kai ga wasan karshe, ko kuma bangaren sabbin hannu irin su Cape Verde, Togo da Burkina Faso.