A karon farko kasar Togo ta samu zarafin tsallakawa zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin nahiyar Afirka dake ci gaba da gudana a kasar Afirka ta Kudu a halin yanzu, bayan ta lashe wasan na jiya Laraba da kasar Tunisia kunnen doki, wato ci 1 da 1 a filin wasa na Nelspriut.
Wannan sakamako da Togon ta samu, ya sanya ta takewa Ivory Coast baya a rukuni na hudu da maki 4, yayin da Ivory Coast din ke sama da maki 7.
Bisa tarihi dai wannan ne karon farko da Togon ta samu damar kaiwa ga wannan matsayi, bayan da a baya ta yi yunkurin hakan har sau 7 ba nasara. Don haka Togo za ta jera tare da ragowar sabbin yanka a wannan zagaye, wato Cape Verde, da Burkina Faso, domin fafatawa da ragowar tsofaffin hannu dake hankoron daukar wannan muhimmin kofi.
Yayin wasan nata da Tunusia, 'yan kallo sun sha mamaki, domin akwai korafin cewa, alkalin wasan Daniel Bennett ya busa wasu abubuwa da ba a gane kansu ba, ciki har da baiwa Tunisia bugun daga kai sai mai tsaron gida sau biyu, ya kuma hana Emmanuel Adebayor irin wannan dama da ya samu cikin wasan, sannan ya baiwa wani dan wasan bayan Togon katin gargadi, bayan kuwa ba shi ne yayi keta ba, cikin mintina 20 na karshen wasan.
Sai dai gazawar Khalid Mouelhi ya sanya kwallo a ragar Togo cikin minti na 78, lokacin da ya buga Penalty na biyu, ya maida hannun agogon Tunisia baya. Don haka sakamakon karshe na wasansu, da kuma kunnen dokin da Algeria ita ma tayi, ya tilasta kasashen larabawan biyu sallama da gasar ta bana.
Sakamakon wannan dauki ba dadi a aka sha, Kocin Togo Didier Six, ya ce ya gamsu da rawar da 'yan wasansa suka taka, yana mai fatan samun karin nasara a wasan su na gaba.
A yayin wasa na biyu tsakanin Ivory Coast da Algeria kuwa, wanda aka tashi ci 2 da 2, daya daga abin da ya ja hankalin 'yan kallo shine yadda kocin Ivory Coast Sabri Lamouchi ya canja 'yan wasa har guda 9.
Haka kuma akwai batun kwallayen da aka sanya a raga, inda dukkanin kwallayen 4, da kungiyoyin 2 suka ci, suka zo ciki mintuna 16 na zagayen wasan na biyu, wato bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Algeria ce dai ta fara sanya kwallo a minti na 64, ta hannun Sofiane Feghouli, mintuna 2 bayan ya canji Ryad Boudebouz, wato dan wasan da ya zubarwa kungiyar tasu bugun daga kai sai mai tsaron gida a zangon wasan na farko. Sai kuma kwallo ta biyu ta hannun Hilal Soudani mintuna 6 bayan ta farko.
Kwallon farko da Ivory Coast ta zura, ta zo ne a minti na 77 ta hannun Didier Drogba, san nan bayan mintina 3 Wilfried Bony ya sharara kwallo a ragar Algerian.
Wasannin farko a zagayen wannan gasa na biyu, za su wakana ne tsakanin Ghana da Cape Verde, da kuma Afirka ta Kudu da Mali a ranar Asabar 2 ga watan nan, sai kuma ranar 3 ga wata da za a taka leda tsakanin Nigeria da Ivory Coast a Rustenburg, da kuma na Burkina Faso da Togo.
Wasan da duk kasar da aka sha, shi ke nan ta yi adabo da gasar ta bana sai kuma karo na ga idan muna da sauran numfashi.