in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya da Burkina Faso sun tsalla zuwa zagaye na biyu a gasar AFCON ta bana
2013-01-30 15:23:05 cri






Wasan da Najeriya ta buga da kasar Habasha ranar Talata 29 ga watan nan, ya zame mata wani abin alfahari, ganin yadda ta samu nasara kan habasha da ci 2 da nema, bayan da wankin hula ya kusa kai ta dare.

Wannan nasara da Najeriya ta samu ta janyowa mai rike da kambin gasar wato kasar Zambia, faduwar bakar tasa, domin kuwa zancen nan da ake yi Zambia na hada komatsanta zuwa gida, bayan da ta tashi nata wasa da kasar Burkina Faso da kunnen doki, wato ci 1 da 1.

Dan wasan Najeriya dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Victor Moses ne dai ya ciwa Super Eagles din kwallaye 2, ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida, cikin minti na 79, ya kuma kara ta biyu a minti na 90. Alkalin wasan dai ya baiwa Najeriya wadannan bugu na "Penalty" ne bayan ya gamsu cewa 'yan wasan Habasha na yiwa takororin nasu, abun nan da a kan kira Sarki ya hana dawa tsaiwa. Laifin da muddin aka aikata shi a kusa da raga, to fa ba shakka bugun daga kai sai mai tsaron gida ne ke biyowa baya.

Yanzu dai Najeriya ce ke biye da kasar Burkina Faso a wannan rukuni na Uku, yayin da Zambia da Habasha kewa gasar ta bana Adabo.

Hakika dai wannan lamari zai dade yana yiwa Zambia ciwo, duba da cewa, wannan ne karo na biyu da kasar dake rike da kambin wannan gasar ta gaza tsallakawa zagaye na biyu, tun bayan shekaru 21 da suka gabata, wato a shekarar 1992, lokacin da kasar Algeria a wancan lokaci ita ma ta fuskanci wannan matsala.

Dangane da nasarar da Burkina Faso ta samu kuwa, kocin ta Paul Put, cewa yayi 'yan wasansa basu bashi kunya ba, kuma sun shiga kundin tarihin bajimta, sun kai kasar su ga burinta na tsallakawa zagayen wannan gasa na gaba.

Yanzu dai Burkina Faso za ta yi wasanta na gaba ne da kungiyar da ta samu nasara a wasan rukuni na Hudu wato Group D, da za a buga tsakanin Togo da Tunusia a gobe Laraba. Yayin da ita kuma Najeriya za ta kwashi 'yan kallo da kasar Cote d'Ivoire a wasa na gaba.

Tuni da kocin Najeriya Stephen Keshi ya sadaukar da nasara da suka samu ga dukkanin 'yan Najeriya a duk inda suke a fadin wannan duniya, yana mai cewa, wannan lokaci ne na farin ciki gare su. Keshi kuma ya kara da cewa ya shiryawa karon battar da za su yi da Cote d'Ivoire, koda yake dai ya ce ba zai farke layar tashi ga manema labaru a halin yanzu ba.

A yayin da Najeriya da Burkina Faso ke darawa, shi kuwa Kocin Zambia Herve Renard, cewa ya yi duk da wannan rana ta bakin ciki ce gare su, a hannu guda burinsu shi ne su samu cikakkiyar nasara, ba wai tsallake wannan zagaye, su kuma gaza daukar kofin ba. Ya kuma jinjinawa 'yan wasansa, da ya ce sun cancanci yabo, idamma akwai wanda za a dorawa laifin rashin nasarsu a cewarsa to shi ne, amma bawai 'yan wasan nasa ba.

Abun jira dai yanzu shi ne ganin yadda wasan gobe Laraba, na rukunin D, wato rukuni na Hudu zai karke, tsakanin Togo da Tunisia, da kuma na Cote d'Ivoire da Algeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China