in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Ghana da Mali sun shiga zagaye na biyu na gasar cin kofin kwallon kafan Afirka
2013-01-29 14:33:22 cri






A jiya ne kasar Ghana ta yi nasarar kaiwa ga wasan gab dana kusa da na karshe wato Quarterfinals, bayan da ta doke Jamhuriyar Nijar da ci 3 da nema, yayin da ita kuma Mali ta tashi kunnen doki ci 1 da 1 da Jamhuriyar demokiradiyar Congo.

Kyaftin din Ghana Asamoah Gyan da Christian Atsu da kuma mai tsaron baya John Boye ne suka zura wa kasar tasu kwalaye, yayin da alkalin wasa kuma ya soke kwallon da 'dan wasan Nijar mai suna Koffi Dan Kowa ya farke mata a wasan da suka yi a filin wasa na Port Elizabeth.

A wasan na biyu kuwa bayan kwallon da Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta zura musu cikin mintuna 3 da fara wasan, yan wasan kasar Mali da suka zo na 3 a gasar ta 2012, sun yunkuro don ganin sun farke wannan kwallo kafin a tafi hutun rabin lokaci a filin wasa na Durban, kuma sun samu wasu damammaki har sau 3 ana dab da kammala wasan, daga karshe dai sun samu sun farke.

Sai dai kyeftin din Mali Seydou Keita ya ce, " wannan nasara da suka samu, abin farin ciki ne matuka garesu, inda 'yan kasar da dakarun Afirka da na Faransa ke fafatawa da 'yan tawaye a arewacin kasar"

Ya ce kasar su na cikin wani yanayi mai wahala a tarihi, 'yan kasar Mali na kokarin kwato arewacin kasar kuma nasarar da suka samu za ta sa jama'a farin ciki, don haka yana matukar alfahari.

Yanzu dai Nijar da jamhuriyar demokiradiyar Congo na shirin tattara faggonsu na komawa gida, bayan da Ghana ta samu maki 7, Mali maki 4 Congo maki 3 kana Nijar na da maki 1 kacal a wasannin da ta buga.

Duk da cewa, Nijar din ba ta yi nasarar kaiwa ga zagaye na gaba na gasar ba, kocinsu Gernot Rohr ya ce, " yana alfahari da 'yan wasansa duk da kashin da suka sha, domin sun nuna juriya kuma akwai haske tare da su a nan gaba.

Dukkan wasannin dai sun kayatar, kuma kowa ce kasa na kokarin ganin ta kai labari a kowa ne wasa da suka buga, sai dai ba kamar gasar shekarar da ta gabata ba, inda akai ta ruwan kwallaye, a wannan karon kowa ya dauki tsauraran matakan ganin, ba a cika ragarsa da kwallaye ba.

Yau kuma kallon ne zai koma rukuni na 3 wato, inda Zambia za ta kara da Burkina-Faso, yayin da Najeriya za ta kara da Habasha.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China