An tashi kunnen doki a wasan da mai masaukin bakin gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka, wato Afirka ta Kudu ta buga da Morocco a ranar Lahadi 27 ga watan nan,inda kasashen biyu suka zira kwallaye bibiyu a ragar juna, matakin da ya baiwa kasar ta Afirka ta Kudu damar zama ta daya a wannan rukuni na daya, ta kuma tsallaka zuwa zagayen gasar na gaba.
Tun da farko dai dan wasan Morocco Issam El-Adoua ne ya fara jefawa kasarsa kwallo a minti na 10 da fara wasan, kafin Afirka ta Kudu ta farke wannan kwallo ta hannun dan wasan ta May Mahlanghu a minti na 71. Kwallo ta 2 da Abdelilah Hafidi ya jefa ragar Afirka ta kudu ta zo ne cikin minti na 82, amma kafin tashi a wasan, sai dan wasan Afirka ta Kudu Siyabonga Sangweni ya farke cikin minti na 87. Aka kuma tashi ko wace kasa na da ci bibiyu.
Wannan wasa ya kayatar matuka, inda kowane bangare ya taka rawar gani, amma dai a iya cewa sa'a ce irin ta kwallo ta sanya Afirka ta Kudun farke kwallon karshe, ana daf da tashi.
Ita ma kasar Cape Verde ta yi nasarar bin sahun Afirka ta Kudu a wannan rukuni, inda a yanzu haka ta samu damar shiga zagaye na biyu na wannan gasa, bayan da ta doke kasar Angola da ci 2 da 1.
Yayin wasan da aka buga a filin wasa na Nelson Mandela Bay a jiya Lahadi, 'yan wasan Angola ne suka fara nuna kwarewa da kai hare-hare, inda suka jefa kwallonsu ta farko cikin minti na 33 da fara wasan ta hannun keftin din su Nando.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne ita ma Cape Verde ta fara yunkurowa, inda a minti na 81 Fernando Varela ya farkewa kasarsa kwallon farko, sai kuma kwallo ta biyu da Heldon ya jefa a ragar Angola a minti na 90, wato ana daf da tashi daga wasan.
Wannan nasara da Cape Verde ta samu, ya sanya ta kasancewa cikin jerin kasashen da za su buga zagayen gasar na biyu. Tuni dai kocin Cape Verde din Lucio Antunes, ya ce sun sadaukar da wannan nasara tasu ga al'ummar kasarsu baki daya. Antunes ya kara da cewa burinsu don gane da wannan gasa ya cika, kasancewar sun samu shiga zagaye na biyu na gasar.
Yanzu dai Cape Verde da Afirka ta Kudu ne za su rankaya zuwa zagaye na Biyu, yayin da Morocco ke hada kayanta zuwa gida, a kuma dai dai lokacin da ake dakon yadda wasa zai kasance tsakanin Ghana da Niger, da kuma Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da Mali a yau Litinin 28 ga wata, wasan da shi ma zai sake fidda karin kasashen da zasu tsallaka zuwa zagayen gasar na biyu daga rukuni na biyu wato B.