Kasar Ivory Coast ta yi waje rod da Tunisiya, bayan ta jefa mata kwallo 3 a raga, yayin wasan rukuni na uku da kulaflikan kasashen biyu suka buga ran 26 ga wata a filin wasa na fadar Bafokeng. Matsayin daya sanya ta kasancewa ta daya, data tsallaka zagayen wasan na biyu, ya kuma tilasawa Tunisiya hada nata ya nata ta koma gida.
Tun da fari dai dan wasan Ivory Coast Gervinho ne ya fara jefa wa kasar tasa kwallo a minti na 21, da taimakon manyan 'yan wasan kungiyar Lancina Toure da Konan, kafin daga bisani shima dan wasan Manchester City Yaya Toure ya jefa tashi kwallo a minti na 87.
Kwallon karshe dan wasan Ivory Coast Didier Ya Konan ne ya sanya ta a zare a minti 90 wato ana daf da tashi daga wasan.
Didier Drogba da ake zaton na cikin manyan 'yan wasan kasar ta Ivory Coast, da zai taka rawar gani a gasar ta bana ya dade a kan benci, inda sai da ya rage mintuna 25 a tashi daga wasan kocin kungiyar tasu ya sanya shi, duk dai da hakan Drogba yace wannan ba wani abun damuwa bane, domin dai duk yadda aka kalli wasan kwalliya ta biya kudin sabulu gare su.
Yanzu dai Tunisiya da a baya aka sanya a matsayi na farko-farko cikin jerin kulaflikan nahiyar Afirka mafiya karfi, kuma ta 22 a duniya, lokaci yayi mata da zata koma gida.
Yayin wasa na biyu kuwa daya gudana tsakanin Togo da Aljeriya, Togon ce ta jefa kwallo 2 a ragar Algeria, Kwallon farko ta hannun Emmanuel Adebayor a minti na 32 da fara wasan, yayin da Dove Wome ya ciwa Togon kwallo ta biyu a minti na 90. Karshen wasan dai Aljeriya ce ta mamaye filin, duk dai da cewa yan wasan ta sun kasa rama kwallayen da aka sanya musu a zare. Tuni dai kocin Togon Didier Six, ya bayyana wannan nasara tasu da sakamako na namijin aikin da 'yan wasan kungiyar suka yi. Shikuwa kocin Algeria Vahid Halilhodzic cewa yayi wannan ranace ta annoba gare su, wanda ta janyo musu jin kunya matuka, kusamma ba zai iya bayyana yadda reshe ya juye da mujiya ba. Bisa hasashe dai Togo na iya tsallakawa zagaye na Biyu na wannan gasa, muddin dai ta samu nasara, koda ta kunnen doki ce yayin wasan ta na gaba da zata buga da Tunusia ranar Laraba mai zuwa.
Yayin da kuma yanzu hankula suka koma ga wasannin gaba wato wasan Cape Verde da Angola, da kuma wasan Morocco da Afirka ta kudu wadanda za'a buga 27 ga wata, ita kuwa Nigeria korafi ta mika ga hukumar shirya wasannin nahiyar Afirka CAF, tama mai bukatar hukumar ta dubi yadda ake nunawa kungiyar ta ta Super Eagles rashin adalci. Ga misali Super Eagles din tace bata gamsu da yadda aka busa wasan ta na farko ran 21 ga wata ba. Haka nan wasanta na ranar Juma'a da Zambia, wanda tace fenaretin da alkalin wasan ya bayar bai dace ba, domin babu wata keta da ta wakana, kuma ma a wajen da'ira ta 16 wancan dan wasa ya fadi, amma alkalin wasan ya busa bugun daga kai sai mai tsaron gida.(Saminu&Ibrahim)