in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeria ta sake tashi kunnen doki yayin wasanta na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ke ci gaba da gudana a halin yanzu
2013-01-26 20:25:42 cri






A wasan da aka yi jiya, Najeriya ta tashi kunnnen doki wato ci 1 da 1 da kasar Zambia, bayan da golan Zambia Kennedy Mweene ya farkewa kasarsa kwallon da aka zura musu a bugun fanareti ana gab da tashi daga wasan abinda ya basu damar tashi 1-1 a wasan da suka yi da Najeriya

Zambia ta samu wannan dama ce bayan alkalin wasa ya ce dan wasan Najeria mai suna Ogenyi Onanzi ya kada Emmanuel Mayuka -hukuncin da ake ganin ya yi tsauri.

Tun a farkon rabin lokaci na wasan ne dai John Mikel Obi na Najeriya ya zubar da wani fanaretin da Najeriyar ta samu a lokacin da ba kasar da ta zura kwallo a ragar 'yar uwarta. Matakin da wasu ke ganin shine ya janyowa Nigeriar rashin samun cikakkiyar nasarar da take nema a wasan rukunin na 3.

A minti 57 ne bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Emmanuel Emenike ya zurawa Super Eagles kwallonta bayan da Ahmed Musa ya garo masa wata kwallo ta gyefen dama, sai dai fanaretin da ake cece-kuce akai ya maidawa Nigeriar hannun agogonta baya.

Wannan wasa dai ya kara nuna yadda Zambia mai rike da kofin a halin yanzu ke fuskantar koma-baya, idan aka yi la'akari da rawar da ta taka lokacin da ta lashe gasar a bara.

Sai dai masu sharhi na bayyana cewa,duk da gargadin da jami'an hukumar kwallon kafan Najeriya suka yiwa 'yan wasan a kwanakin baya, sakamakon rashin tabuka abin azo a gani a wasansu da Burkina-Faso, da alamun '"ba ta canja zane ba", ganin yadda 'yan wasan Zambia suka yi ta kai zafafan hare-hare a gidan 'yan Najeriya.

A daya wasan da aka buga a rukunin na 3 kuwa Burkina Faso ta lallasa Ethiopia da ci 4-0, yanzu ke nan Burkina ce ke kan gaba a rukunin da maki hudu. Hakan dai na nuna cewa wannan rukunin a bude yake, inda dukkan kasashen hudun na da damar tsallake wa zuwa zagaye na gaba.

Awasan farko da Najeriya ta yi da kasar Burkina-Faso,sun tashi ne ci 1da1, haka itama Zambia a wasanta na farko da Habasha,sun tashi ci 1 da 1.

Sai dai bayan minti talati da fara wasa alkalin wasa ya kori golan Burkina-Faso Abdoulaye Soulama,saboda ya kama kwallo a wajen layin da aka shata masa, amma duka da rashin dan wasan guda, 'yan wasan sun ci gaba da taka leda yadda ya kamata.

Bayan minti 34 ne da take kwallo, dan wasan Burkina-Faso mai suna Alain Traore ya zura wa kasarsa kwallo sannan bayan minti 16 ya kara wata kwallon, kana a minti na 79 Djakaridja Kone ya kara kwallo ta uku, sannan sai kwallon Jonathan Pitroipa wadda ta zamo ta hudu.

Wani abin mamaki shi ne, an dan dakatar da wasan na dan wani lokaci, yayin da wani dan kallo ya kutsa kai cikin filin wasa daga shi sai kamfai, kafin daga bisani jami'an tsaro su cafke shi.

Wannan dai sakamako na nuna cewa Burkina Fason ce ke gaba a wannan rukuni da maki 4, yayin da Nigeria da Zambia ke biye da maki bibiyu, sai kuma Habasha dake kasan jadawalin da maki daya tak.

A yau ne kuma Ivory coast zata kara da Tunisia yayin da Algeria za ta kece raini da Togo, a wasanni na biyu cikin rukunin D. (Saminu Alhassan/Ibraim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China