'Yan wasan Black stars na kasar Ghana sun samu nasara kan kungiyar wasan kwallon kafar Mali, da ci daya da nema yayin wasan rukuni na biyu da aka buga ranar Alhamis 24 ga watan nan. Dan wasan tsakiyar Black Stars Mubarak Wakasu ne dai ya dada kwallo a ragar Mali cikin minti na 38 da take wasan, bayan ya samu damar bugun daga kai sai mai tsaron gida. Dan wasan Mali Tamboura ne dai ya yiwa Emmanuel Agyemang-Badu keta, al'amarin daya janyo bada bugun daga kai sai mai tsaron gidan.
Ko da yake dai a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu ga kungiyar ta Ghana, a hannu guda wasu daga 'yan kallo sun bayyana rashin gamsuwarsu da irin rawar da Ghanan ta taka, akwai ma wadanda ke ganin da 'yan wasan sun yi amfani da kwarewarsu yadda ya kamata da watakila wasan yafi armashi.
Sabanin irin wannan ra'ayi, tsohon dan wasan kungiyar ta Black Stars Ibrahim Sunday cewa ya yi ya gamsu da irin hobbasan da 'yan wasan suka yi, ko da yake dai shi ma na ganin wajibi ne su zage damtse yayin wasansu na gaba. A nasa bangare dan gaban kungiyar Ablade Kumah ya bayyana farin cikinsa da yadda wasan nasu ya kasance, tare da fatan wasan gaba zai kayatar fiye da na wannan lokaci.
Wannan dai shi ne karo na 2 da a baya bayan nan Ghana ta samu nasara kan kasar ta Mali cikin wasanni 3 da suka buga a manyan wasanni ciki hadda na gasar cin kofin Nahiyar ta Afirka da ya gabata a bara a Gabon da Guinea Konakri. Yanzu dai Ghana nada maki 4 a wasannin ta 2, za kuma ta kara da Niger, yayin wasanta na 3 a wannan rukuni na B, ranar Litinin mai zuwa a filin wasa na Nelson Mandela Bay dake Port Elizabeth.
Dangane da wasan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da Niger kuwa, kasashen biyu sun tashi canjaras babu ci, wanda hakan ya baiwa Niger damar samun maki 1, na kuma farko tun fara wannan gasa. Wasan wanda masu kallo da dama ke ganin bai kayatar ba, ganin yadda kungiyoyin biyu suka kasa sanya kwallo a raga, ya kasance wani mizani na awon nasarar da ake hange ga kungiyoyin biyu, musamman ma a wannan rukuni na biyu da tuni Ghana ta yiwa kamun kazar Kuku. Cikin manyan hare haren da aka gani yayin wasan dai akwai wata kwallo da Modibo Sidibo na Niger ba buga amma ta daki karfen raga ta dawo. A kwai kuma kwallon 2 da Dieumerci Mbokani ya buga amma mai tsaron gidan Niger Daouda Kassaly ya hana su shiga raga. Yanzu kuma yayin da Niger za ta kara da Ghana a wasanta na gaba, ita kuwa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da ta kece reni ne da Mali, wadda ta kwashi kashinta a hannu yayin wasanta da Ghana, bayan da ta samu nasara a wasanta na farko tsakaninta da Niger.
Bisa kididdiga dai wasan na ranar Alhamis shi ne na 7 a jerin wasannin da aka tashi kunnen doki, cikin jimillar wasanni 12 da aka rigaya aka buga.
Yanzu dai hankula sun koma ga wasannin Nigeri da Zambia, da ma wasan Burkina Faso da Habasha da za su gudana a yammacin Jumma'ar nan 25 ga wata.