in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai masaukin bakin gasar cin kofin nahiyar Afrika ta lallasa Angola da ci biyu da nema
2013-01-24 16:55:16 cri






Wasan da ya gudana ranar Laraba 23 ga watannan a filin wasa na Moses Mabhida, tsakanin kasar Afirka ta kudu dake matsayin mai masaukin baki a gasar cin kofin nahiyar Afirka na bana, da takwarar ta ta Angola yayiwa Afirka ta Kudun dadi, domin kuwa ta samu zarafin lallasa Angolan da ci 2 da nema. Matakin da ya bata damar kasancewa ta daya a rukunin na A da maki 4. Kocin kungiyar ta Bafana Bafana Gordon Igesund wanda ya sauya 'yan wasa 5 yayin wasan bai samu damar sararawa ba, har sai lokacin da dan wasan sa Siyabonga Sangweni ya jefa kwallon farko a ragar Angola a minti na 30 da fara wasan, kafin daga bisani Lehlohonolo ya sake kara kwallo ta 2 a minti na 62.

Tuni dai Ministan wasannin kasar Fikile Mbabula ya taya kungiyar ta Bafana Bafana murnar nasar da suka samu, yana mai cewa sun taka rawar gani, ya kuma kara da cewa zasu ci gaba da samun dukkanin irin tallafi da goyon bayan da suke bukata daga tsagin gwamnatin kasar. Kulaf din kasar ta Afirka ta kudu dai da a wasan sa na farko ya tashi kunnen doki maras ci da Cape Verde, zai buga wasan sa na gaba ne da Morocco ranar Lahadi mai zuwa a birnin Durban. Baya ga hukumar wasannin kasar, shima wani tsohon dan wasan Nigeria Pascal Karibe Ojigwe, ya jinjinawa kungiyar ta Bafana Bafana, yana mai cewa wannan nasara tasu, zata basu damar taka babban matsayi a wannan gasa. Ojigwe yayi hasashen cewa Afirka ta kudun na iya kaiwa ga wasa na ukun na karshe wato "quarter Finals".

Yayin wasa na biyu kuwa daya gudana tsakanin kasar Cape Verde da Morocco, Cape verde ce ta fara sanya kwallo a zare ta hannun dan wasanta Platini a minti na 35 da fara wasan, a wani lamari da ya kusa baiwa Moroccon tarin mamaki, sai dai cikin mintina 78, wato ana daf da kammala wasan ne kuma dan wasan Moroccon Youssef El-Arabi ya farke kwallon da aka sanya musu, bayan Abdelaziz Barrada ya sanya masa wata kyakkyawar dama gaban sa. A yanzu dai haka Cape Verde da Moroccon ne ki biye da Afirka ta Kudu da maki bibiyu a jadawalin rukunin na farko, inda kuma Angola ke can kasa da maki daya tak.

Yanzu kuwa hankula sun fara karkata ga wasannin ranar 24 ga wata, inda kasashen dake rukuni na biyu wato Ghana da Mali, da kuma Niger da Janhuriyar dimokaradiyyar Congo zasu fafata a tsakanin su. Mali dai ce a kan gaba a wannan rukuni bayan da ta jefawa Niger kwallo daya mai ban haushi a wasan su na farko, sai kuma Ghana da Janhuriyar dimokaradiyyar Congo da suka tashi kunnen doki a wasannin da suka bubbuga na farko, yayin da Niger ke karshen jadawalin, duba da yadda ta rasa koda maki daya a wasan ta na farko.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China