in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manazarta harkokin wasanni na sanya ido ga irin rawar da kulaf din kasar Ivory Coast, da manyan 'yan wasan sa za su taka a bana
2013-01-23 16:13:51 cri
Kulab din kasar Zambia na cikin manyan kulaflika 10 a nahiyar Afirka da ake wa kallon zakaru a 'yan shekarun baya-bayan nan, ganin yadda ya shige gaba wajen lashe gasar cin kofin nahiyar daya gabata a bara, koda yake a bana ya fara wasan sa na farko da kunnen doki. Amma a hannu guda kulaf din kwallon kafar Ivory Coast da a baran ya zamo na biyu, na da matukar farin jini da kwarjini a idon 'yan kallo, dama masu fashin baki a harkar wasanni.

A bana wasu na ganin lokaci ne da kulaf din ya kamata ya nuna matsayin sa na abin kaunar masu kallo, in kuwa hakan ta faskara tofa babu shakka, sunan sa na iya sauyawa da wani abun daban. Idanuwa za kuma su raja'a kan gwarzon dan wasan kasar Didier Drogba, wanda sau 5 ke nan yana halartar wannan gasa, kuma ke da kambin dan wasan Afirka mafi bajimta da kwarewa a yanzu. Duk da wannan nasara tasa yana matukar kishirwar daga wannan kofi na nahiyar Afirka. Dan wasan mai shekaru 34 da haihuwa, wanda kuma yayin gasar wasannin bana ya jefa kwallaye 56 a raga cikin wasanni 90 daya buga, ana ganin akwai yiwuwar ya taka muhimmiyar rawa a bana, domin gasar da ake yi a yanzu haka na iya zame masa ta karshe da zai bugawa kulaf in na kasar sa, saboda yawan shekaru. Baya ga Drogba ragowar 'yan wasa kamar Yaya Toure da Wilfreid Bony na iya taka leda yadda ya kamata.

" Akwai dar-dar da sanya ido a kammu, amma hakan bazai razana mu ba" inji kocin kungiyar ta Ivory Coast Sabri Lamouchi.

Idan kuma muka kalli ragowar kulaflikan nahiyar masu karfi, zamu iya cewa kasar ta Ivory Coast na da babban kalubale a gabanta. Kasashe irin su Ghana, da Mali, da Morocco, da Algeria dama Nigeria na dakon dauki-ba-dadi da takwarorin su, yayin wasu ke kebe Ghana wadda ta dauki wannan kofi shekaru 30 da suka gabata a matsayin wadda a wannan karo zata motsa kwanjin ta domin dawo da nasarar ta ta baya.

Ita ma mai masaukin baki wato Afirka ta kudu zata yi duk mai yiwuwa domin samun nasarar da 'yan kasar zasu yi alfahari da ita, Mali koda yake dai bata taba daukar wannan kofi ba, ana ganin yawan 'yan wasan ta dake manyan kulaflikan Turai, na iya bata karfin gwiwar da take fata. Har wa yau a daya bangare akwai kasashen Congo, da Habasha, da Tunisia, da janhuriyar dimokaradiyyar Congo da a baya suka taba daukar wanna kofi, suma ana ganin ba zasu bari a bar su a baya ba. Rana dai bata karya inji Bahaushe. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China