Bugu da kari kocin Super Eagles din ya ce burin cimma wannan manufa ne ma ya sanya shi sanya 'yan wasa masu karancin shekaru cikin kungiyar a wannan karo, da ma rage yawan tsoffin 'yan wasa kamar dai yadda ake gani a jerin sunayen 'yan wasan da suke bugawa Nigeriar kwallo a gasar AFCON ta bana. Ko da yake dai wasu daga masu nazarin kungiyar sun yi mamakin rashin sanya 'yan wasa irin su Peter Odemwingie, da Obafemi Martins, cikin wadan da za a je da su gasar ta Afirka ta Kudu a bana.
Nigeriar dai na cikin kasashen da suka yi suna matuka a fagen taka leda, musamman ma a nahiyar Afirka, sai dai a baya-bayan nan ta sha fama da matsaloli da dama, ciki hadda gaza samun damar zuwa gasar cin kofin nahiyar da ya gabata. Lamarin da ya sanya 'yan kallo da masu sharhi sanya ido a wannan karo, domin ganin ko za ta sauya zani.
A hannu guda kuma wannan wata dama ce ga sabon kocin kungiyar wato Stephen Keshi, ta ya nunawa duniya irin kwarewar sa, da sanin makamar aiki, a matsayin sa na kocin gida, wanda kuma a baya ya taba bugawa kungiyar ta Super Eagles kwallo, yayin da kungiyar ta lashe wannan kofi na nahiyar Afirka a shekarar 1994, ta kuma taka rawar gani a gasar cin kofin duniya daya gudana a kasar Amurka. (Saminu)