A wannan lokacin da muke jiran wasan da za a taka tsakanin kungiyoyin 2, ya kamata mu dan yin bayani kan kungiyar Zambiya, domin mu san cocinta, da kwararrun 'yan wasanta, sa'an kuma mu shirya kallon rawar da zata taka a wannan gasa mai kayatarwa .
A gasannin cin kofin Afirka da aka shirya a baya, kungiyar Zambiya ta taba shiga zagayen karshe karo 15, inda ta zama zakara karo guda, wato a shekarar 2012, sa'an nan ta kasance ta biyu a shekarun 1974 da 1994. Yanzu kungiyar tana matsayi na 34 a jadawalin kwararrun kungiyoyin kwallon kafa na duniya da hukumar FIFA ta fitar.
Cocin kungiyar Zambia wani dan kasar Faransa ne mai suna Herve Renard, wanda ya jagoranci kungiyar wajen lashe kofin Afirka a bara, abin da ya ba shi damar zama coci mafi kwarewa a nahiyar Afirka na waccan shekara. A shekarar 2010, ya taba barin Zambia don ya zama mai horar da 'yan wasan kungiyar Angola, daga inda kuma ya tashi zuwa Algeria, domin aiki a kulob din USM Alger. Haka kuma Renard ya taba aiki a karkashin wani kocin dan Faransa wanda ake kira Claude Le Roy a nan kasar Sin, haka kuma ya taba horar da 'yan wasan kungiyar kasar Ghana.
In kuwa muka koma batun wasu daga kwararrun 'yan wasan dake kungiyar kwallon kafar Zambia, da farko za a fara tunawa da Chris Katongo, wanda ya kasance kyaftin din kungiyar. Dan wasan mai shekaru 30 a duniya, yana buga gaba ne, kuma yana taka leda a kulob din Henan Jianye dake nan kasar Sin. A dukkanin gasannin cin kofin Afirka guda 4 da suka gabata, ya sanya kwallaye cikin raga, kana a shekarar 2007, an daukaka shi zuwa matsayin saja a rundunar sojojin kasar Zambiya, bayan da ya jefa kwallaye 3 cikin raga a jere, yayin da kungiyarsa ke karawa da kungiyar Afirka ta Kudu don neman samun damar shiga gasar cin kofin duniya.
Ban da Katongo kuma, sai Jacob Mulenga, wani dan wasan gaba mai shekaru 28 a duniya. Ko da yake dai shi wannan dan wasa bai samu damar taka leda a kungiyar Zambiya ba, a lokacin da ta samu kambi a bara sakamakon raunin da ya ji. Daga baya ya samu murmurewa don haka ya koma kungiyar, yayin da ake ganin yiwuwar mika shi ga wani kulob dake kasar Birtaniya, wato daga kulab din ketare da yakewa wasa na kasar Holand wato (FC Utrecht). A baya ma dai ya taba tsallakawa daga kulab din Copperbelt don shiga kasar Faransa a lokacin da yake da shekaru 20 a duniya. Ya dade yana taka leda a rukunin kwararru mataki na 2, wato (lig-2), kafin ya samu daukaka zuwa FC Utrecht din, wadda ke kasar Holland a shekarar 2009.
Sai dai kamar yadda masu iya magana su kan ce, mai laya ya kiyayi mai zamani, ya kamata mu mai da hankali kan wasu 'yan wasa matasa masu kwarewa dake cikin kungiyar Zambia, kuma masu kanan shekaru ga misali, Emmanuel Mayuka. Duk da cewa yana da shekaru 22 ne kacal da haihuwa, amma yana taka leda a Southampton ta kasar Birtaniya a matsayin dan wasan gaba. Ya kasance dan wasan mafi karancin shekaru a kungiyarsa ta gida wato Zambia, yayin gasar cin kofin duniya na shekarar 2008 da kungiyar ta halarta. Kafin haka ya taba shiga gasar zakarun matasan duniya a shekarar 2007 a matsayin daya daga 'yan wasan kasar ta Zambia, yana kuma cikin fitattun 'yan wasa matasa da kasar ta zaba domin a ba su horo na musamman, sa'an nan a sanya su kai tsaye cikin kungiyar kasar.
Manazarta wasannin motsa jiki na ganin cewa, dadilin da ya sa kungiyar Zambiya ta lashe kofin Afirka a shekarar 2012 shi ne, kasancewar kasar ta yi shekaru tana kokarin hada kwararrun 'yan wasa don kafa wata kungiyar kwallon kafa ta kasa, kana a lokacin ba a kallon kungiyar a matsayin wadda za ta iya lashe kofi. Sai dai a wannan karo, za a iya ganin wani sauyin yanayi kan wannan kungiya, domin ta kasance mai kare kambi, wadda kuma sauran kungiyoyi za su nuna cikakken karfi kanta, a yunkurin su na kwace wannan kofi da kowa ke fatan samu. (Bello Wang)