in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen kwadebuwa da tunusia sun lashe wasannin rukuni na hudu(D), na gasar CIN kofin nahiyar Afrika dake gudana.
2013-01-23 15:53:37 cri






Kasar Ivory Coast ta lallasa kasar Togo da ci 2-1 a wasan rukuni na hudu wato Group D na gasar cin kofin kwallon kafan Afrika dake gudana a Afirka ta kudu.

Ivory Coast ta samu kwallonta ta farko ne daga hannun Yaya Toure a minti takwas da fara wasa. Yayin da a minti na arba'in da biyar kuma Togo ta rama kwallon, ta hannun Jonathan Ayite wato ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Kana a minti na tamanin da takwas, ana dab da tashi ne kuma Yaya Toure ya cillo bugun free-kick, shi kuwa Gervinho dake bugawa kulaf din Arsenal kwallo ya jefa ta a zare.

Da wannan nasara yanzu Ivory Coast ce ta daya a rukunin na hudu, wato Group D, inda Tunusia ke biye mata.

A wasan da aka yi tsakanin Tunisia da Algeria kuwa, Tunisia ce ta samu galaba akan Algeria da ci 1 da nema, a dai wasan rukuni na hudu wato Group D na gasar cin Kofin Afrika.

Dan wasan Tunisia Youssef Msakni shi ne ya ciwa kasarsa kwallon a na dab da tashi daga wasan cikin minti na 90.

Duk da kashin da suka sha,'Yan wasan Algeria dai sun fara taka leda sai dai ba su sami nasarar yin amfani da damar da su ka samu ba, a bayan minti na 29 inda kwallon da Islam Slimani ya buga ta doki saman karfen ragar gidan Tunisia.

Wannan nasara da Tunisia ta samu ta bata damar kasancewa a bayan Ivory Coast wadda ta ci Togo 2-1 a wasan da suka yi a wannan rukuni.

A wani labarin kuma,hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta gayyaci Kocin Super Eagles na Najeriya dangane da sakacin da suka yi a wasansu da kasar Burkina-Faso. Shugaban hukumar Aminu Maigari ya shaida wa manema labarai cewar ya gayyaci Stephen Keshi da sauran masu horar da 'yan kwallon kasar ta Najeriya ne,don su yi bayani a kan abin da ya janyo kasar ba ta taka rawar gani

A cewar Aminu Maigari, sun gana daga baya kuma suka gayyaci jami'ai da ke horas da 'yan wasan don nuna musa rashin jin dadinsu, game da rawar da suka taka, mun kuma nuna musu wuraren da ke bukatar gyara, kafin wasansu na gaba.

Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, "bayan tattaunawar da muka yi da jami'an kungiyar ta Najeriya, sun yi alkawarin zage damtse don ganin an samu nasara a wasansu da Zambia da ke tafe, kuma sun ji dadin abin da muka nuna musu, inda suka ce za su yi duk abin da ya dace a wasanmu da Zambia"

Tuni dai kKyaftin din Nigeriar Joseph Yobo ya bayyanawa manema labaru rashin gamsuwarsu, da irin yadda suka yi sakaci, yayin wancan wasa da ya gabata.

Har yanzu Najeriya na kokarin ganin ta sake lashe kofin kwallon Afrika tun bayan kofin da ta lashe a shekarar 1994, bayan da ta doke kasar Zambia.

Kuma a ranar Juma'a za ta sake fafata wa da Zambia a gasar ta bana.

Ita ma kasar Zambian mai rike da kofin, ta tashi 1-1 ne a wasanta na farko da Ethiopia.

Su ma a nasu bangare magoya bayan kungiyar kwallon kafar kasar Zambia, bayyana rashin gamsuwa suka yi da yadda wasan kungiyar na farko ya kasance, suna masu fatan kungiyar tasu, za ta lallasa Nigeria a wasan ranar 25 ga wata dake tafe.

Bisa ga yadda wasan ke gudana,alamu na nuna cewa,manyan kasashe na shan mamaki,yayin da suma kananan kasashen ke nuna cewa, su fa ba kanwar lashe ba ne, don haka kusan komai na iya kasancewa,wato dai "ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare".

A yau ne kuma kasashen da ke rukuni na daya wato A, wadanda suka hada da kasashen Afirka ta kudu mai masaukin baki, Angola, Cape-Verde da kuma Morocco, za su dawo fagen fama, inda a wasan farko, Afirka ta kudu za ta kara da Angola yayin da Morocco za ta fafata da Cape-Verde.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China