in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tashi kunnen doki a wasannin zango na 3 na gasar cin kofin Afirka
2013-01-22 16:27:25 cri






Kamar dai wasannin zangon farko da suka wakana ran bude gasar cin kofin nahiyar Afirka dake gudana a Afirka ta Kudu, suma wasannin ranar Litinin 21 ga wata an tashi kunnen doki, sai dai a wannan karon akwai ci, wato dai wasan Zambia da Habasha an tashi ci daya da daya, haka ma wasan Nigeria da Burkina Faso shi ma an tashi daya da daya.

Yayin wasan farko da aka yi a filin wasan Mbombela na Nespruit, kungiyar Habasha ta kai hare hare, amma babu nasara. Ciki hadda babbar damar bugun daga kai sai mai tsaron gida, a minti na 23 da fara wasan, wadda kwararren dan wasan kasar Saladain Said ya zubar. Ita ma Zambia wato mai rike da kanbin gasar ta samu danammaki da dama, ciki hadda wadda Adane Girma ya ajiye, a minti na 48 kafin tafiya hutun rabin lokaci, wadda kuma nan take Collins Mbesuma ya jefa ta a raga.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma dan wasan Habasha Adane Girma ya farke kwallon ga kungiyarsa, a minti na 65. Cikin abubuwan da suka auku cikin wannan wasa akwai korar mai tsaron gidan Habasha Jemel Tassew da alkalin wasan yayi a minti na 30 da fara wasan, bayan da alkalin ya same shi da laifin aikata keta. Duk dai da yadda wasan ya kaya 'yan wasan Habasha da magoya bayansu, sun rika murna da nuna farin ciki tamkar sun samu cikakkiyar nasa. 'yan wasan Habasha kamar su Saladain Said, da Wadi Degla da kuma mai tsaron gidansu da aka sallama sun taka rawar gani yayin wannan gasa.

A bangaren Zambia kuwa 'yan wasa irinsu Mbesuma, da Chris Katongo, da Addis Hintsa, da Mumuka Mulenga suma sun baje basirar su yayin wasan.

Sai kuma wasa na biyu tsakanin kungiyar Nigeria da Burkina fasa. Shima dai kunnen dokin aka tashi. Cikin kuma hare hare da aka kai akwai na Ahmed Musa wanda ya buga kwallo saman raga cikin minti na 12, da kwallon da Emenike ya daga, amma Ideye Brown ya sanya kai kwallon kuma ta fita a minti na 15, koda yake dai Elderson Echiejile na bayansa, yana jiran ko ta kwana. A minti na 65 shi ma Ikechuku da ya sarrafa wata kyakkyawar kallo ya auna ta waje. Kwallon da ake gani ya kamata ya jefa cikin zare ba tare da wata wahala ba. An kuma kori Efe Ambrose a minti na 74, saan nan Uche ya sake barar da wata damar, ta hanyar sheka kwallon saman raga, bayan da Mikel Obi ya tace masa kwallo, a minti na 80

A nata bangare kungiyar Burkina Faso ta kai wani hari a minti na 17 ta hannun dan wasa Jonathan Pitroipa, amma Widfried Dah ya buga kwallo jikin raga. Haka nan a minti na 32 sun kusa farke kwallonsu amma Djakaridja Kone da Aristide Bance suka yi karo, don haka suka rasa wannan dama. A Minti na 48 ma an so a sanya kwallo a raga, amma Moumoni Dagano ya kasa sanya kai dai dai bayan da Pitroipa ya dago masa kwallo. Bayan an fara fidda rai da sauyawar wasan ne, cikin mintunan karshen wasan 94, Alain Traore ta hannu Pitroipa ya samu wata kwallo da nan take ya dada ta a raga.

Yayin da hakan ke faruwa wasu 'yan Nijeriar nuna rashin jin dadin su suka yi, sakamakon rashin wuta da ya hana su kallon wasan da kungiyar ta Super Eagles ta buga. Wakilinmu dake Abuja babban birnin tarayyar kasar Danladi yace wasu daya zanta dasu sun bukaci hukumar samar da wutar lantari da ta dada gwazo, domin samar musu da wuta yayin da Nigeriar ke taka leda, domin su samu ganewa idanun su yadda take wakana.

A wani batun kuma mahukuntan kasar Zambia sun alkawartawa 'yan wasan su kyautar kudi har dalar Amurka 20,000 kowanen su, muddin dai suka sake lashe wannan gasa a bana. Ministan wasannin kasar Chishimba Kambwili ne ya bayyanawa 'yan wasan wannan alkawari, yana mai nanata kiran da fadar shugaban kasar ta Zambia tayi musu tun da fari, na su dada kaimi, wajen daukaka martabar kasar su ta haihuwa.

Dama dai a baya ma yayin gasar data gabata, sai da mahukuntan kasar ta Zambia suka baiwa kowane dan wasa kyautar dalar Amurka 59,000. Yanzu dai ana iya cewa dabara ta rage ga 'yan wasan kungiyar ta Zambia, dama kocin ta Herve Renard.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China