in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi wa 'yan wasan Zambia alkawarin makuden kudade muddin suka kare kofin da suka lashe
2013-01-22 11:20:06 cri
Jaridar kasar Zambia mai suna Zambia Daily Mail, ta bayar da rahoto a ranar Litinin cewa, an yiwa 'yan wasan kasar alkawarin makuden kudaden alawus muddin suka kare kofin kwallon kafan Afirka da suka lashe a shekarar da ta gabata, inda 'yan wasan za su samu dala 90,000 muddin suka kare kofin a gasar da aka fara ranar Asabar a kasar Afirka ta kudu.

Ministan wasanni na kasar Chishimba Kambwili ya shaidawa 'yan wasan a kasar Afirka ta kudu cewa, idan har suka kai ga wasan karshe, kowane dan wasa zai samu dala 20,000.

A ranar Litinin ne, kasar ta Zambia ta kara da kasar Habasha a rukuni na 3 wato C. Sauran kasashen da ke wannan rukunin sun hada da Nigeria da kuma Burkina-Faso.

'Yan wasan sun samu dala 59,000 kowane, yayin da suka lashe kofin a shekara ta 2012, bayan da suka doke 'yan wasan kasar Ivoary-Coast a bugun daga kai sai mai tsaron gida da ci 8 da 7.

A ranar Lahadi ne shugaban kasar ta Zambia Micheal Sata ya sake shaidawa 'yan wasan da su ba marada kunya, a lokacin da ya ziyarce su a Nelspruit bayan da ya halarci bikin bude gasar a ranar Asabar, inda ya bayyana tabbacin cewa, 'yan wasan za su kare kofin da suka lashe.

Tuni dai kocin kungiyar Herve Renard, ya bukaci 'yan wasan da kada su raina kowace kungiyar da za su kara da ita a matakin rukuni.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China