Wakilinmu dake Abuja ya ce ya zanta da wasu mazauna birnin wadanda suka tabbatar da cewa, a tsakiyar ranar ta litinin har zuwa dare, babu wutar lantarki, amma bayan gasar cin kofin Afirkan da aka buga tsakanin kungiyar Nijeriya da Burkina Faso, an ba da wutar lantarki tad an wani lokaci , sa'an nan kuma aka sake daukewa. Wani mazaunin birnin na Abuja malam Bello, ya nuna rashin jin dadinsa, sabo da bai samu damar kallon wasan ba sabo da rashin wuta. Malam Bello ya ba da shawawra ga hukumar da ke samar da wutar da ta tabbatar da baiwa jama'a wutar yayin wasan, koda ba za a samu wutar a ragowar lokuta ba.
Danladi, wakilin CRI daga Abuja, Nijeriya.