Gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2013 da a yanzu ke gudana a kasar Afirka ta Kudu ta fara armashi, bayan da kungiyar kwallon kafar kasar Mali ta ci wasan ta na farko, inda ta lashe Niger da ci daya mai ban haushi.
Yayin wasannin farko da suka gudana ranar Asabar 19 ga watan nan tsakanin kulaflikan kasashen Afirka ta Kudu da Cape Verde, da kuma na Kasar Angola da Morocco dake rukuni na farko wato "Group A", dukkanin wasannin an tashi ne babu ci. Matakin da ya sanya 'yan kallo da dama, nuna rashin gansuwar su da wannan sakamako, musamman ma daga kasar Afirka ta Kudu, wadda ke matsayin mai masaukin bakin gasar.
Sai dai wannan yanayi ya sauya ranar Lahadi 20 ga wata, inda bayan kungiyoyin Ghana da Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun tashi kunnen doki da ci biyu da biyu. Wasan Mali da Niger ya sauya alkiblar gasar, inda dan wasan Mali Seydou Keita ya jefa kwallo a zare, a na kimanin mintuna 6 a tashi daga wasan. Tsohon dan wasan kungiyar Bercalonan yayi kyakkyawan amfani da kwallon da Diawara Fousseiny ya cillo masa, inda nan take ya dada ta a zare. Koda yake dai dama kulaf din kasar ta Mali bisa tarihi yafi na Niger din karfi, duba da yadda ya halarci gasar har sau 8 ita kuma Niger ta 2, duk da hakan 'yan wasan Niger din sun taka rawar gani musamman ma mai tsaron gida Daouda Kassaly yayi matukar kokarin kare farmakin da
Mali ta rika kai musu, yayin da suma 'yan gaban kungiyar ta Niger suka rika kai hare-hare yadda ya kamata.
Yanzu dai hankula sun koma ga wasannin ranar Litinin 21 ga wata, inda ake saran ganin sakamakon wasannin Nigeria da Burkina Faso, da kuma wasan Zambia da habasha. Wasannin da kowannen su ake fatan zai kayatar matuka, a wannan rukuni na 3 wato "Group C". Nigeria dai nada kwararrun 'yan wasa na gida dana waje, ta kuma taba daukar kofin wannan gasa har karo 2, wato a shekarun 1980 da kuma 1994, haka nan ta halarci gasar sau17, inda ita kuma Burkina Faso ta halarci gasar sau 9. Itama dai Burkina Faso nada 'yan wasa kwararru, ana kuma saran zata taka muhimmiyar rawa a wasan na yau.
Don gane da wasan Zambia da Habasha kuwa shima wasane da zai kayatar, domin Zambia da ta halarci gasar sau16, itace ke rike da kambin gasar, ko zata iya sake rike wannan kambi a bana? tambayar da manazarta da dama ke furtawa kenan. Itama Habasha da a baya ta halarci gasar har sau 10 ana saran za tayi iya kokarin ta, domin taka rawar data kamace ta. Duba da irin muhimmancin da kasashe 16 masu halartar gasar ke sanyawa ga batun samun nasa yayin wannan gasa mai farin jin. Bahaushe dai kance ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare.(Saminu da Ibrahim)