in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sako daga malam Musa Adamu Abubakar a Gombe, tarayyar Nijeriya
2013-01-21 10:27:00 cri
Na rubuto muku wannan wasika don na jinjina muku bisa irin ayyuka da kuke gabatarwa ba dare ba rana. Ku sani irin wannan aiki naku ya ratsa kowane lungu a wannan duniya tamu,don haka ni da membobina na kungiyar JEYRALA muke muku fatan alheri a kowane lokaci. Ku sani a kullum burinmu shine ganin ci gabanku a duniya, don haka muke fatan kamar yadda kuke hulda da abokanku za ku ci gaba ba tare da wata matsala ba. Ku sani mun shigo shekarar 2013 da kafar dama tare da fatan alheri ga dukkan al'umma, don haka muke fatan CRI za ta dubi ayyukanta na baya, wajen kuskure- ta gyara, duk da mun san babu wani kuskuren. Bayan haka, kamar yadda Allah ya daukaka wannan gidan radio wato CRI wajen samun masu sauraro da yawa a kowane kwana ta duniya. To, kada fa ku yi sake wajen mantawa da su, ballantana wasu sabbi da suka cusa kansu wajen sauraron shirye-shiryenku, kada ku yi watsi da su, su ma ku dama da su don ku ga kamun ludayinsu. CRI, a wannan shekarar ta 2013, ku yi kokarin ganin kun cika dukkan alkawari da za ku dauka, domin ganin shekarar tana da albarka.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China