A ran Asabar 19 ga wata ne shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya jagoranci bikin bude gasar cin kofin nahiyar Afirka na bana, yayin bikin da ya samu halartar dimbin jama'a 'yan kasar, da ragowar baki, da ma 'yan kallo daga sassan duniya daban daban, wanda kuma aka gudanar a filin wasa na Soweto dake birnin Johannesburg, shugaba Zuma ya ce, gasar ta bana za ta taka muhimmiyar rawa wajen sake inganta dankon zumunta dake tsakanin kasashen dake nahiyar Afirka.
Bayan bikin bude gasar, an gudanar da wasannin farko tsakanin kasashen Afirka ta Kudu da Cape verde, da kuma Angola da Moroco, wasannin da aka tashi babu ci.
Wannan dai gasa da ke a matsayin mafi girma dake gudana a nahiyar ta Afirka za a ci gaba da yinta har izuwa ran 10 ga wata mai zuwa.(Saminu)