Kamar kowa ya sani, jama'ar Nijeriya suna kaunar yin wasannin motsa jiki a filaye musamman kwallon kafa, kuma sun son kallon wasannin kwallon kafa, sun bayyana cewa, wasannin kwallon kafa na kwafin Afirka sun zama wata muhimmiyar dama gare su da su ga 'yan wasa na kwallon kafa na kasar. Jama'a sun bayyana cewa, suna fata kungiyar Nijeriya za ta iya samu maki mai kyau a wasannin.
Kafin budewar wasannin, shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya ya sa kaimi ga 'yan wasa da su yi kokari domin kawo kyakkyawar martaba ga Nijeriya, da kuma nuna matsayinta na wata babbar kasa mai girma a duk nahiyar Afirka.(Danladi)