A wannan lokacin da muke ci gaba da dakon fara gasar cin kofin Afirka, ya kamata mu mai da hankali kan yanayin da wasu kungiyoyin dake da damar lashe gasar suke ciki, mu kwatanta su, ta yadda za mu iya hasashen wace ce daga cikinsu ta fi kusanci da lashe wannan kambi. A yau za mu duba kungiyar Nijeriya, inda za mu ayyana 'yan wasanta, da sakamakon da ake sa ran ganin ta samu.
Kungiyar Nijeriya, wadda ta taba shiga zagayen karshen na wannan gasa ta cin kofin Afirka har karo 16 a tarihinta, ta taba lashe kofin a shekarar 1980 da 1994, kana ta zama ta biyu a shekaru 4 wato shekarun 1984,1988,1990,da 2000.
A halin yanzu kungiyar tana matsayi na 52 a jadawalin kwararrun kungiyoyin kwallon kafa na duniya da hukumar FIFA ta fitar.
Mai horar da 'yan wasan kungiyar Najeriya, Stephen Keshi, ya kasance kyaftin din ta, a lokacin da kungiyar ta lashe kofin Afirka a karon da ya gabata, wato a shekarar 1994. Keshi, da a yanzu ke da shekaru 51 a duniya, ya taba halartar gasannin cin kofin Afirka guda 5, kana a yayin gasar ta 3 ya je a matsayin mai horar da 'yan wasan kungiyar Najeriya.
Yanzu kuma bari mu dubi wasu 'yan wasa kwararru dake cikin kungiyar ta Nigeria. Ga misali, Victor Moses, mai shekaru 22 da haihuwa, ya kasance dan wasan tsakiya. Haka kuma a yanzu haka yana bugawa kulob din Chelsea dake kasar Birtaniya kwallo. A lokacin da yake da shekaru 11 da haihuwa ya yi kaura daga birnin Ikko na Tarayyar Najeriya zuwa Birtaniya, inda ya taba shiga gasannin 'yan kasa da shekaru 21. A 2012, ya samu shiga kungiyar Super Eagles ta Najeriya a karon farko, a wasan da kungiyar ta yi da Rwanda a watan Fabrairu, daga baya ya sauya sheka daga kungiyar Wigan zuwa ta Chelsea. Daga shigar sa Super Eagles ya ci kwallaye 2 ga kungiyar.
Ban da shi Moses ma akwai John Obi Mikel, mai shekaru 25 a duniya, wanda shi ma yake taka leda a kungiyar Chelsea a matsayin dan wasan tsakiya. Duk da cewa, a kulob din Chelsea a kan sa shi a baya, amma a kungiyar Naijeriya akan ba shi karin damar kai hari wato buga gaba. Mikel ya fara taka leda a kungiyar Najeriya a lokacin da yake da shekaru 18, don haka yanzu ya riga ya zama wani tsohon hannu da Super Eagle din ta buga wasanni 14 tare da shi, wadanda suka gudana a gasannin cin kofin Afirka guda 3. Sai dai bai samu damar shiga gasar cin kofin duniya da ta gudana a Afirka ta Kudu a shekarar 2010 ba sakamakon rauni da ya samu.
To yanzu kuma sai Joseph Yobo, dan wasan baya mai shekaru 32. Yana kuma cikin FC Fenerbahce ta kasar Turkiya. A matsayin kyaftin din kungiyar Naijeriya, ya kasance dan wasan mafi dadewa yana takawa Super Eagles leda, ganin ya riga ya shiga cikin gasannin cin kofin Afirka guda 6. Haka kuma, a cikin 'yan wasan bayan kungiyar wadanda yawancinsu sabbin jini ne shi kadai ya taba shiga gasar cin kofin Afirka.
Dangane da kungiyar Najeriya mun san ko da yaushe ta kasance cikin kungiyoyi mafiya karfi, wadanda ke da damar lashe kofin nahiyar. Sai dai, a gasar da ta gabata wadda ta gudana a kasashen Equatorial Gini da Gabon, ta gaza fitowa daga zagaye na 2. Haka kuma, wasu na cewa kungiyar ta yanzu ba ta kai ta da ba, ganin 'yan wasan ta dake taka leda a kungiyoyi masu karfi na kasashen Turai sun ragu. (Bello Wang)