in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambiya ta Soke Wasan Sada Zumunci, Domin Hutar Da 'Yan Wasanta
2013-01-18 16:53:36 cri
Yayin da wasu kungiyoyin ke ci gaba da wasannin sada zumunci, gabanin fara gasar cin kofin nahiyar Afirka, ita kuwa kungiyar kwallon kafar kasar Zambia, kuma mai rike da kambin gasar soke wasan ta na sada zumunci da Namibia tayi, domin baiwa 'yan wasanta damar hutawa, kafin fara dauki-ba-dadi da ragowar kulaflikan da zasu shiga gasar.

A cewar shugaban hukumar lura da wasannin kwallon kafar kasar Namibia John Muinjo, kulaf din Zambia ya bayyana musu kurewar lokaci, a matsayin dalilin fasa buga wasan da a baya aka tsara gudanarwa ranar Talatar data gabata.

Zambia dai bata samu nasara a wasannin sada zumunci da tayi da kasashen Tanzania da Angola ba, ta kuma yi kunnen-doki da Morocco, za kuma ta buga wasan farko a rukunin C tare da kasar Habasha ranar 21 ga watan nan a Nelspruit. (Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China