Hukumar aikin gaggawa ta kasar Afrika ta Kudu ta ba da rahoton hattara dake nuna cewa, za'a samu ruwa kamar da bakin kwarya a wasu yankunan kasar tun daga ranar Jumma'a da yamma, kwana guda kafin bude gasar cin kofin kwallon kafa na CAN karo na 29. Ma'akatar daidaita bala'u ta riga ta samu labari, in ji hukumar aikin gaggawa ta Tshwane dake birnin Pretoria a cikin wata sanarwa.
Hukumar Tshwane ta bukaci ba da kashedin farko kan ruwan sama masu karfi da za'a samu a wannan mako. Cibiyar hasashen yanayi ta Afrika ta Kudu ta sanar da hukumomin daidaita bala'u cewa, akwai yiyuwar samun ruwan sama masu yawa. Ruwan saman zai iyar kawo illa ga CAN, babbar gasar kwallon kafa mafi janyo hankali a Afrika da za'a fara ranar Asabar har zuwa 10 ga watan Fabrairun shekarar 2013.
A cewar wannan sanarwa, yankunan arewa maso yammacin kasar da suka hada da Gauteng, KwaZulu-Natal, Limpopo da Mpumala za su fara samun ruwan masu karfi a wajen karshen ranar Jumma'a zuwa ranar Lahadi.
Kasar Afrika ta Kudu, ita ma kasa ce dake fama da ambaliyar ruwa, a yankin KwaZulu-Natal, a kalla mutane 10 suka mutu kana wasu dama suka jikkata a yayin wasu ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a cikin watan Disamban shekarar 2012. (Maman Ada)