in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar CAF ta yaba da shirye-shiryen gasar kwallon kafa ta CAN
2013-01-15 12:01:14 cri

A yayin da ake ta cigaba da samun suka kan shirye-shiryen gasar cin kofin kwallon kafar Afrika CAN ne, kungiyar kwallon kafa ta Afrika (CAF) ta nuna yabo a ranar Litinin ga kokarin da hukumomin kasar Afrika ta Kudu suka yi domin karbar bakuncin wannan muhimmiyyar gasar kwallon kafa ta Afrika.

"Muna nuna yabo matuka tare da nuna godiya ga kwamitin shirya wannan gasa na Afrika ta Kudu (COL) kan jan namijin aikin da ya yi.'' in ji sakatare janar na CAF, mista Amrani a birnin Johannesburg. Kalamin mista Amrani ya kasance wani babban maki ga shirye-shiryen da Afrika ta Kudu take na wannan gasa da ya kamata a fara daga ranar 19 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Febrairu.

Kwamitin COL ya fuskanci korafe korafe na tafiyar hawainiya wajen sayar da tikitoci da nuna kasawa wajen shirya tallace tallacen janyo hankali. A makon da ya gabata, an nuna cewa, kimanin tikitoci dubu 300 ne bisa jimillar dubu 500 kawai aka samu shigar da su kasuwa.

Amma duk da haka, an samu shigar da wasu nau'in tikitoci, kamar na bude bikin gasar da na rufewa gaba daya sun kare, in ji COL.

Haka zalika mista Amrani ya bayyana cewa, tikitocin wasan taka leda na bude gasar tsakanin 'yan kungiyar Bafana Bafana ta Afrika ta Kudu da 'yan wasan kasar Cap-Vert sun kare. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China