in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta tura sojoji zuwa Mali don yaki da 'yan ta'adda
2013-01-14 16:56:13 cri






A farkon wannan wata, an shiga rudani a kasar Mali da ke yankin yammacin nahiyar Afrika, kuma dakarun dake adawa da gwamnatin sun ci gaba da ta da zaune-tsaye, lamarin da ya sanya shugaban kasar Faransa Francois Hollande yanke shawarar tura sojoji zuwa kasar ta Mali, don taimakawa gwamnatin wucin gadi ta kasar wajen yaki da dakarun dake adawa da gwamnatin kasar wadanda ake alakantawa da aikata laifukan ta'addanci. A ranar 13 ga wata, sojojin sama na kasar Faransa sun ci gaba da jefa boma-bomai ga matsugunan 'yan tawayen cikin jerin kwanaki ukku da sojojin Faransa suka shafe a kasar Mali. Bisa labarun da aka bayar, an ce, nan ba da dadewa ba, kasashe Nijer, Senegal, da Burkina Faso da ke makwabtaka da Mali, su ma, za su tura sojoji don taimakawa gwamnatin wucin gadi ta Mali

Daga watan Maris na bara, lokacin da aka yi yunkurin juyin mulkin soji a kasar Mali, yanayin da ake ciki a kasar ya shiga rudani, gwamnatin wucin gadin kasar na rike da wasu yankuna ne kawai, yayin da 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayin Islama da ke adawa da gwamnatin suka mamaye galiban yankunan kasar, a yanzu haka 'yan tawayen na dada kutsawa yankunan da ke da nisa kilomita daruruwa da birnin Bamako, hedkwatar kasar Mali tun farkon watan Janairu na bana. Bayan da gwamnatin Faransa ta amince da rokon taimako da gwamnatin wucin gadi ta Mali ta bayyana ne dai, ta yanke shawarar tura sojoji zuwa kasar, musamman a matsayin Faransa na wadda ta reni kasar ta Mali, kuma sabo da kasar Faransa ta taba zama kasar da ta reni kasashen Afrika da dama, a kan yi mata da lakabi da suna "Sojojin Afrika", a wannan karo ma, bayan da yanayin da ake ciki a kasar Mali ya dada tabarbarewa, ta dauki matakin habaka rawar da take takawa a kasashen Afrika, da kara kwarjininta, Faransa ta shugabanci tura sojoji zuwa Mali.

Game da batun kasar Mali, Faransa na sahun gaba wajen tuttura sojoji, abin da ya sa jama'a da dama tunawa da yanayin da aka shiga ciki a shekaru 2 da suka gabata a kasar Libya, wato Faransa da ke karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy, ita ma ta zama a sahun gaba wajen gudanar da ayyukan soji a kasar Libya, yanzu, kuwa koma bayan tattalin arziki a kasar Faransa, ya sanya shugaban kasar mai ci yanzu Francois Hollande da ya yi rabin shekara kacal yana aiki neman goyon baya daga al'ummar kasar, tare da fata jama'ar za su karkata hankalinsu zuwa kasashen waje, kuma yana fatan kara samun goyon baya don cimma nasarar yaki da ta'addanci a kasashen waje.

A ranar 13 ga wata, ministan tsaro na kasar Faransa Jean-Yves Rod Lyon ya bayyana ra'ayinsa game da tura sojoji zuwa kasar Mali a kafofin yada labaru da ke da farin jini sosai, yana mai cewa, dalilin da ya sa Faransa ta tura sojoji zuwa kasar Mali, shi ne domin yaki da ta'addanci, da kare abokanta, kana da kare Faransawa da ke zauna a kasar. Bisa umurnin da shugaban Hollande ya bayar, an ce, yanzu, jiragen saman yaki da jiragen sama masu saukar ungulu da dama sun isa kasarta Mali, don share fagen fara aiki, yanzu, hakan nan yawan sojojin kasar Faransa da ke kasar Mali ya kai sama da 400, ministan tsoro ya kiyasta cewa, wannan yaki zai dau makwanni ko watanni. Ko da yake, yanzu, ana matakin fara shi, amma lokaci bai yi ba da za a fara batun kawo karshensa ba, amma gwamnatin Faransa tana fata za a farfado da zaman lafiya a kasar, kana kuma, za a kori dakarun da ke adawa da gwamnatin daga yankunan kudancin kasar.

Sabo da akasarin 'yan tawaye na kasar Mali, na da alaka da kungiyoyin ta'addanci, sabo da haka ne, Faransa ta kara daukar matakai don magance hare-haren da za su iya kaiwa, kuma ta kara jan kunnen jama'a da su yi hattara, alal misali, a titin CHAMPS ELYSEES da hasumiyar Tour Eiffel, aka kara daukar matakan sintiri. Game da tura sojoji a kasar Mali, wasu daga jama'ar kasar Faransa sun nuna damuwarsu, inda wasu suka bayyana cewa, kamata ya yi Faransa ta taimaki kasashe renonta don magance ta'addanci, amma batun na iya janyo ramuwar gayya, kana kuma wasu jama'ar kasarta Faransa sun bayyana cewa, kamata ya yi Faransa da kasashen duniya su dauki matakin soji tare, ban da wannan kuma, sabo da yanzu Faransa ita ma tana fama da matsalar kyautata zaman rayuwar al'umma, idan ba a warware wannan matsala ba, ta tsunduma cikin rikicin Mali, kila ma da kyar za ta iya farfado da tattalin arzikinta.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China