Idan ba a manta ba, kungiyar ta taba nuna karfinta a gasar cin kofin duniya da ta gudana a kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2010, inda ta shiga zagaye na kusa da na karshe. Sai dai ta kasa samun ci gaba a gasar, sakamakon yadda aka lashe ta a zagayen bugun daga kai sai mai tsaron gida.
A gasar AFCON na wannan karo, kungiyar Ghana tana cikin rukunin B, tare da Mali, Niger, da DR Congo. 'Yan wasan kungiyar sun riga sun tashi zuwa wata cibiyar horaswa dake Abu Dhabi (Babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa) a ranar 4 ga wata. Kafin haka kuma mai horar da 'yan wasan kungiyar Kwesi Appiah ya gabatar da jerin sunayen 'yan wasan da za su je Afirka ta Kudu a madadin kasar, ciki hadda fitattun 'yan wasa irinsu John Panstil, Asamoah Gyan, Suley Muntari, da Anthony Annan.
Yanzu haka jama'ar kasar Ghana masu sha'awar kwallo kafa da 'yan wasa matasa na kasar suna Allah-Allah a fara taka leda, ganin 'yan wasan kungiyar kasar da ake kiransu 'Black Stars' wato 'bakaken taurari' a Hausance, na iya dawowa gida da kofin Afirka, matakin da zai iya zama tamkar karya wani dabo ne, da ya hana su samun nasara a shekaru 30 da suka wuce.
Sai dai a ra'ayin masu fashin baki a fannin wasanni, domin kyautata makomar kasar ta fuskar kwallon kafa, ya kamata a kara mai da hankali kan horar da matasan kasar masu sha'awar taka kwallon. Kamar yadda wani mai sharhi mai suna Michael Adjei ya bayyana, a cewar sa kafin a samu wata kungiyar kwallon kafa mai karfi, tilas ne a gina wani tushe mai inganci, wanda zai kasance wani tsarin koyar da fasahar taka leda. Adjei yace, duk wata nasarar da kungiyar kasar ta samu ko zata samu, muddin dai tsarin kulob din bai canza ba, baza a iya samun wata makoma mai haske a fannin kwallon kafa ba.
Hakika dai, a halin da ake ciki, jama'ar kasar Ghana su ma sun fara nuna damuwa kan harkar kwallon kafa ta kasar, ganin yadda kungiyoyin kasar na 'yan kasa da shekaru-17 da 'yan kasa da shekaru -20, wato 'yan wasan da shekarunsu ba su wuce 17 da 20 ba, suka kasa samun damar shiga manyan gasannin kasa da kasa, haka zalika, yunkurin kungiyar 'yan wasan da shekarunsu ke kasa da 23 ta ci tura, a kokarinta na neman shiga wasannin Olympics da ya gudana a binin London na kasar Birtaniya a bara. (Bello Wang)