KULAF DIN SHOLA AMEOBI YA HANA DAN WASAN SHIGA JERIN WADANDA ZASU BUGAWA NIGERIA KWALLO A GASAR NAHIYAR AFIRKA DAKE TAFE
Ga alama dai kulaf din Newcastle ya ci nasarar fafatawar da ya yi da kungiyar Super Eagle ta Nigeria, don gane da batun hana dan wasan sa Shola Ameobi damar dawowa gida, don bugawa kulaf din Nigeriar gasar nahiyar Afirka da za a fara nan da 'yan kwanaki. Inda a yanzu mahukuntan kungiyar ta Super Eagle suka zare sunan Ameobi daga jerin 'yan wasan da zasu buga masa kwallo, bayan da jagoran Newcastle Alan Padew yayi kememe wajen hana dan wasan shiga jerin takwarorin sa na Nigeriar, duk kuwa da barazanar da kocin Super Eagle Stephen Keshi yayi, ta kai kulaf din na Newcastle kara gaban hukumar FIFA. Bugu da kari kakakin kulaf din na Super Eagle Ben Alaiya, ya bayyana cewa, Ameobi ya ki daukar wayar mai horas da 'yan wasan na Super Eagle don haka babu abin yi da ya wuce sauya sunan sa da wani dan wasan na daban.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku